Fitattun ‘Yan Nijeriya Da Ranar Haihuwarsu Ta Zagayo

Gwamnan Bauchi

Daga Basira Sabo Nadabo,

SANATA BALA MUHAMMAD

 

Gwamnan Jihar Bauchi mai ci, Sanata Bala Mohammed, an haife shi 5 ga watan Oktoban 1958. Shi ne ya yi ministan Abuja daga shekarar 2010 zuwa 2015. Ya yi sanata daga 2007 zuwa 2010. Dan jam’iyyar PDP ne da ta kasance babbar ‘yar adawa a Nijeriya

 

Bala Abdulkadir Mohammed an haife shi a Alkaleri. Ya yi karatun gaba da sakandire a jami’ar Maiduguri daga 1979 zuwa 1982 inda ya samu digiri a fannin Turanci (English).

Ya yi aiki a ma’aikatu da dama ciki har da ta cikin gida, ma’adanai, lantarki da karafa da sufuri da kuma sufurin jiragen sama.

 

OLUSEGUN MIMIKO

 

Olusegun Mimiko. An haife shi a ranar 3 ga watan Oktoban shekara ta 1954, ya samu nasarar zama Sanata a karkashin Jam’iyyar Labour, a mazabar Ondo ta tsakiya a zaben shekara ta 2019. Dan siyasa ne da ya yi Gwamnan Jihar Ondo, daga Fabarairun shekara ta 2009, zuwa Fabrirun shekarar 2017. Shi ne na na farkon da ya yi mulki sau biyu a jihar ta Ondo kuma farkon gwamna a jam’iyyar Labour a Nijeriya.

 

HARUNA BABANGIDA

 

Haruna Babangida, tsohon dankwallon Nijeriya ne wanda aka haifa ranar 1 ga watan Oktoba shekara ta 1982. Babangida shi ne na takwas a cikin iyalansu. Sannan kani ne ga Tijjani Babangida.

An haife shi a Kaduna, ya fara kwallonsa a kungiyar Shooting Stars, kafin ya rattaba hannu a kwantiragi da kulob din Ajad yana da shekara 13 da haihuwa. Sannan ya tafi Barcelona. Yayin da ya cika shekara 15, Babangida ya fara halartar manyan wasanni na kulob-kulob har zuwa matakin da ya buga wa Nijeriya wasanni da dama.

 

 

CHIDERA EZEH

 

Chidera Kennedy Ezeh, an haife shi 2 ga watan Oktoba shekara ta 1997). Shi ma dan kwallon kafa ne na Nijeriya da ke bugawa a Portugal a kulub na ‘yan kasa da shekara 23 da haihuwa.

Kwararre ne kuma ya halarci gasar Segunda Liga a ranar 20 ga watan Nuwamban shekara ta 2016 a Braga B.

Ya lashe gasar cin kofin duniya na shekara ta 2013 na ‘yan kasa da shekara 17 da haihuwa. Yas amu nasarar jefa wa Nijeriya kwallo a raga a karawar kusa da karshe da aka yi da Sweden.

 

Exit mobile version