FMAN Ta Yaba Wa Manoman Alkama A Jigawa 

Daga Munkaila Abdullah,

Kungiyar masu sarrafa fulawa ta Nijeriya FMAN ta jinjinawa Manoman Alkama a jihar Jigawa bisa kwazonsu wajen noma Alkamar akan lokaci.

Shugabar Kungiyar ta FMAN, Sarah Huber ce tayi wannan yabo a yayin bikin Kungiyar na shekara wadda aka gabatar a garin Maje dake karamar hukumar Taura a jihar ta Jigawa.

Sarah Huber ta kuma yi kira gabe Manoman dasu kara kaimi wajen bunkasa noman Alkama domin tallafawa kudurin gwammati na samarda wadataccen abinci a wannan kasa.

Haka kuma ta bayyana cewa, a yunkurin Kungiyar tasu ta FMAN wajen bunkasa noman Alkama a wannan kasa sun zabi jihohi uku da suka hadarda Jigawa, Kano da kuma jihar Kebbi yadda suka gudanar da ayyuka da dama domin bunkasa noman na Alkama.

Sannan tace, a jihar Jigawa sun kuma zabi kananan hukumomi biyar wadda suka hadarda kananan hukumomin Taura, Ringim, Birnin Kudu, Malam-madori da Kafin Hausa akan wannan shiri.

Shugabar ta kuma kara da cewa, kimanin manoma dubu biyar ne suka sami horon noman Alkama gamida wasu kuma sun kimanin 700 wadanda aka baiwa bashin takin zamani tareda kyautar ingantaccen Irin Alkama.

Haka kuma ta ce, Kungiyar tasu ta samar cibiyar binciken Don samarda ingantaccen iri a garin Ringim tareda hadin kwiwar cibiyar bincike ta Lake Chad Research Institute.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa a madadin Manoman da suka amfana da wannan shiri, shugaban Kungiyar Manoman Alkama ta kasa Dr Saddik Ahmad, ya baiwa Kungiyar tabbacin cewa Manoman Zasu rubanya yunkurinsu domin samarda wadatacciyar Alkama a wannan kasa.

Exit mobile version