Connect with us

LABARAI

Forestry Research Institute Ta Shirya Taron Kara Wa Juna Sani A Zariya

Published

on

A cikin makon da gabata ne hukumar Forestry research institute of Nigeria ta shirya taron karwa juna sani ga manoma a bubban dakin taro dake cibiyar nazarin aikin gona dake jami’ar Ahmad Bello Zariya (I.R.A).

A farkon taron an sami halartar manyan baki daga cibiyoyin nazarin aikin gona da masana a bangaren ilmin gandun daji da sarakuna da shugabanin kungiyoyin manoma na bangarori da dama bubban bako a wannan waje shine minisata muhalli na kasa Alhaji Ibrahim Usman Jibril sai wakilin shugaban jami’ar ABU daya rufa mashi baya a wajan bude wannan taro.

Taron dai an shiryashine don baiwa manoma ilmin sabbin dabarun aikin noma da raya itatuwa a fadin kasa baki daya don samun mafita ga canjin yanayi da ake samu a halin yazu.

Alhaji Bawa ’Yargada Sarkin Noman Gundumar Rigasa Kaduna da Buhari Lawal dukkansu mahalatta taronne sun shaida jaridar Leadership A yau cewa, tabbas sunyi farin ciki da wannan taro domin suna samun dabarun noma Wanda da hakan na amfanar da kasa baki daya domin duk basirar da suka samu to suma sukan yadashi ne ga sauran manoma a fadin kasa baki daya hakan yasa da yawan matasa suna samun aikin da zasu iya rike kansu da Kansu su kuma manoma na samun damar fadada sana’ar tasu ta noma tare da samun riba mai gwabi.

Shi ma ministan da yake amsa tambayoyin manema labarai akan ko menene makasudun wannan taron sai ya kada baki yace, “ Samawa kasa mafita akan canjin yanayi da ake samu a wannan zamani tare da magance matsalar zaman kashe wando ga matasanmu ta hanyar basu ilmin aikin gona da raya itace da muhimmancinsa game rayuwar dan Adam wanda kuma wannan gwamatin ta mai girma shugaban kasa Muhammad Buhari ke ta kira a kansa tare da kashe makudan kudi don tabatar da hakan a fadin kasa baki daya hakan yasa nayi farincin ganin dubban manoman da suka sami zuwa wannan taro don haka ina kira ga dukkan mahalatta wannan taro da su zama jakadu na Kwarai”

Dakta Adeshehu shine bubban darafta na wannan cibiyar a nasa jawabin ya nuna godiya ne ga minista daya bar komi ya halacci wannan taro yace hakan zai karawa wannan cibiya kwarin guiwar gabatar da aiyukanta data saba na bayar da dabarun aikin gona ga al’umar kasa baki daya.

Daraktan ya ce, su na matukar samun nasara akan dukkan abubuwan da sukasa a gaba kuma yayi kira ga gwamnati da cewa da bukatar ta kara kaimi wajan taimakon da suke bayarwa don karfafa cibiyoyi da nazarce-nazarce da cibiyoyi ke gudanarwa a duk fadin kasa baki daya.

Karshe yayi kira ga wanda suka sami damar samun zuwa wannan taron da su zama jakadu na gari yayi fatan yadda aka fara lafiya Allah yasa a gama lafiya.

 
Advertisement

labarai