FRSC Ta Shawarci Direbobi Kan Tukin Ganganci A Lokacin Damina

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa, wato FRSC ta gargadi direbobi da su guji tukin ganganci musamman a lokacin daminar nan, a yayin da hadari ya hadu a gari ko ruwan saman ya sauka.

Kwamandan na jihar Ogun, Clement Oladele, shi ne ya yi wannan gargadin a yau Asabar a garin Abeokuta. Oladele ya nemi direbobin su sani cewa ruwan sama yana rufe hanya a yayin da kake tuki, inda ya bukaci direbobin da su guji gudu a yayin da ruwan sama ya sauka.

Sannan ya nemi da su rika tukin hankali suna kallon gaban su, domin bishiyoyi na iya karyo was u fado, da kuma falwaya da sauran abubuwan da ka iya haifar da hadari. Oladele ya tabbatar da cewa; direbobi su rika bincikar motocinsu kafin fara tukinsu.

 

Exit mobile version