Hussaini Yero" />

FRSC Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 139 A 2020 A Jihar Zamfara

Hukumar kare hadura ta Kasa reshen Jihar Zamfara (FRSC),ta bayyana cewa, mutane dari da talatin da tara ne suka rasa rayukan su, sakamakon haduran ababen hawa a shekara da ta gabata ta 2020,a cikin Jihar Zamfara.

Kwamandan hukumar na Jihar Zamfara, Idris Aliyu Fika ne ya bayyana haka, a lokacin da yeke tattaunawa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

“Idris Fika ya bayyana cewa,a shekarar da ta gabata 2020 , anyi hadura dubu daya da dari uku da tara,mutane dari bakwai da talatin da takwas ne suk samu raunuka , mutane dari da talatin da tara suka rasa rayukan su, mutane dari da ashirin da bakwai magidanta ne sai kuma mata goma sha biyu da kanann Yara uku.inji Kamanda Fika.

Da ya ke bayyana matsalolin da suka haifarda haduran , Kwamandan Fika ,ya bayyana cewa,yawan gudu bisa kima da kuma daukar Fasinja da ya zarce iyaka da kuma Aron hannu da masu ababen hawa keyi ya haifar da wadannan haduran,a wannan Jihar ta Zamfara.

Idris Fika ya kuma tabbatar da cewa,a wannan shekara ta 2021 , hukumar FRSC,tayi shiri na musamma ga masu ababen hawa a wannan Jihar,dan cigaba da  wayar da kansu,akan sani ka’idar tuki da yadda zasuceci rayukan al’umm da ke hannun su.kuma lallai hukumar FRSC ba zata lamunci sakaci da direbobi masu tunkin ganganci da Aron hannu da kuma lodin wuce iyaka ba a cikin Jiha ta Zamfara.

Kuma hukumar zata kaddamar da shirin tsaftace ababan hawa da yaki da masu tukin ganganci da Aron hannu da masu sanya gilashi meduhu a motar su dan suna kawo barazana ga harkar tsaro .kuma wannan shirin zamuyi shine tare da hadin gyuwar jami’an tsaro.

A karshe Kwamandan Fika yayi kira ga Fasinjoji da su kasance masu tsawata ma Direbobi a lokacin da suke tuki,idan ya yi badai daiba su tsawata masa.dan ceton rayuwar su.kuma su kasance masu amfani da rigakafin annobar Korona ,na sanya takunkumi a koda yaushe a loacin da suke cikin mota.

 

 

Exit mobile version