Connect with us

LABARAI

FSARS Ta Ceto Dan Shugaban APC Da Aka Yi Garkuwa Da Shi A Borno

Published

on

Jami’an tsaro masu yaki da yan fashi da makami (Federal Special Anti -Robbery Squad) da ke Maiduguri a jihar Borno, sun ceto yaro dan shekara hudu, dan shugaban jam’iyyar APC a jihar Borno, Kashim Bukar-Dalori, wanda wasu suka sace ranar Larabar da ta gabata.

Rahotanni sun nuna cewa wata mata ce wadda wasu bayanai suka ce tana da alaka da gidan, inda ta hada kai da wadanda sace yaron a makaranta, da kimanin karfe 1:00 na rana.

Tun daga bisani dai, kwamishinan yan-sandan jihar Borno, Demian Chukwu, ya bayyana cewa rundunar su ta daukin gaggawa wajen binciken kwakwaf kan wadanda suka yi garkuwa da karamin yaron.

Wata majiya ta sanar da cewa, jami’an tsaron sun yi sa’ar damke mutum uku daga cikin masu garkuwar a birnin Maiduguri da Kano, a ranar jumu’a, a kan hanyar su ta zuwa karbar kudin fansa; naira miliyan 20, da suka bukata daga iyayen yaron.

“Binciken ya gano wadanda ake zargi da garkuwa da yaron, wanda ya hada da mace dayan wadda ta bukaci a mika kudin fansar, naira miliyan 20 a Kano, wadda jami’an namu suka cafke”.

“An ceto karamin yaron wanda aka ajiye shi a ‘Albarka Hotel’ da ke Maiduguri, a hannun wata mata, kuma an riga an mika shi ga iyayen sa, wanda bayan karbar kudin fansar ne kuma shi ne sai jam’an mu na IRT, a can Kano suka kama matar. Wanda kuma nan take, bayan damketa sai ta gaya mana inda suka boye yaron. Kuma bisa ga wannan ne ya jawo muka tattaro jami’an mu inda muka zagaye wajen don ceto yaron”.

“Matar ita ce wadda ta je har makarantar tare da dauke karamin yaron.”

Edet Okon, babban jami’in hulda da jama’a na rundunar yan-sandan jihar Borno, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

“Ina tabbatar maka da cewa, an ceto karamin yaro dan shugaban jam’iyyar APC a jihar Borno, wanda aka sace tare da damke wadanda suka yi garkuwar dashi. Har wa yau kuma, ana gudanar da bincike a kan wadanda ake zargin, kuma za a gurfanar dasu a gaban kuliya”.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: