Muhammad Maitela" />

FUGA: Farfesa Waziri Za Ta Gaji Farfesa Andrew Haruna

A makonni biyu da su ka gabata, hukumar gudanarwar jami’ar gwamnarin tarayya da ke Gashuwa, jihar Yobe su ka amince da nada Farfesa Maimuna Waziri a matsayin sabuwar shugabar jami’ar (bice Chancellor), wadda za ta gaji Farfesa Andrew Haruna, wadda ita ce ta uku kuma mace ta farko a jerin wadanda su ka shugabanci jami’ar.
Farfesa Waziri, yar asalin Gashuwa kuma kwararriya, ita ce mataimakiyar shugaban jami’ar mai barin-gado kan sha’anin mulki (Deputy bice Chancellor Admin) na tsawon shekaru hudu, mace hazika kuma jajartacciya wadda ta bayar da gudumawa wajen ci gaban da jami’ar ta samu da nasarori a fannoni daban- daban, wanda kuma ma’aikatan jami’ar ke yi wa fatan ci gaba da kyawawan ayyukan da Farfesa Andrew Haruna ya samar a FUGA.
A taron da shugaban jami’ar mai barin-gado ya yi da manema labarai a ranar Alhamis, ya bayyana wasu daga nasarorin da ya samu tun daga lokacin da aka nada shi a matsayin shugaban jami’ar Fuga. Wanda ya fara da bayyana yabo tare da jinjina ga hukumar gudanarwar jami’ar, tsohon shugaban jami’ar, Farfesa Shehu Abdulrahman, da sauran manya da kananan ma’aikata a jami’ar, a matsayin wadanda su ka bayar da cikakken goyon baya da gudumawa wajen cimma nasarorin da ya samu a jami’ar.
A hannu guda kuma ya bayyana matukar godiyar sa dangane da cikakken goyon bayan da gwamnatin jihar Yobe ta bashi a tsawon zamansa na shugaban jami’ar Fuga, musamman Gwamna Mai Mala Buni wanda ko kowane lokaci kofarsa a bude take wajen bayar da kowane irin goyon baya wajen ci gaban jami’ar. Haka zalika da taimako karfin gwiwar da ya samu daga masarautun jihar Yobe baki daya, musamman Sarkin (Mai) Bade, Alhaji Abubakar Umar Suleiman, wadanda ta hanyar bazarsu ya cimma nasarorin da ya samu.
Farfesa Haruna ya bayyana cewa ya fara aiki a matsayin bice Chancellor a jami’ar cikin watan Fabarairun 2016, a lokacin da take jaririya tare da tsangayoyi uku (Facults): tsangayar ayyukan noma, tsangayar Arts, al’amurran gudanarwa da rayuwa (Management and Social Science) sai na kimiyya (Science) hadi da kwasa-kwasai 23.
Ya bayyana cewa, bayan zuwansa jami’ar ya tsayu wajen ganin cewa baki dayan wadannan kwasa-kwasai 23 a jami’ar sun samu amincewar hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC), wanda 18 an riga an kammala amincewa dasu, wanda 5 kuma su ka samu amincewar wucin-gadi. Wanda ko shakka babu wannan namijin kokari ne.
Bugu da kari kuma, ya nuna yadda kyakkyawar alaka tsakanin ofiahin shi da sauran bangarorin jami’ar hadi da ma’aikatanta ya gudana ba tare da wata tangarda ba, a tsawon wannan lokaci da ya dauka ya na shugabantar jami’ar. Ya ce wannan ya samu ne ta dalilin matakan da ofishin nashi ya dauka wajen kokarin sauke nauyin da ya hau kansa ta fannin hadin gwiwa da kowane bangare, kokari wajen yi wa ma’aikatan da su ka dace ayi musu karin girma da karfafa musu domin kyautata ayyukan su da makamantan hakan.
“A wannan tsakanin, mun yi kokarin kara wa jimlar ma’aikatan jami’ar Fuga 91 girma, wadanda su ka kunshi malaman jami’s 22, manyan ma’aikata a fannin gudanarwa (Admin) 43, kwararrun ma’aikata 26 hadi da wasu kananan ma’aikata a wannan bangaren. Haka kuma da karin wasu malaman jami’a 5 wadanda muka kara darajarsu zuwa matsayin Farfesoshi, tare da wasu 4 a matsayin ‘Readers’, wanda yanzu Fuga tana da farsesoshi 8.”
Da ya karkata zuwa manyan ayyuka a jami’ar, ta hanyar hukumar tallafi ga manyan makarantu ta kasa (TetFund) ta aiwatar hadi da wadanda yanzu haka suna ci gaba da gudana a Fuga, ya ce daga ciki akwai na dakin karatu wanda hukumar ta basu kayan aiki, littafai da makamantan su, wanda yanzu haka dakin karatun yana aiki kowace ranar Allah.
“Haka kuma, TetFund sun gina sabon dakin gwajin kimiyya tare da kayan aiki (Central Laboratory) gina babban dakin karatu mai daukar dalibai 1000, ofishin shugaban jami’ar na wucin-gadi, ofisoshin malaman jami’a, dakunan kwanan dalibai da wajen wasanni da kammala gine-ginen tsangayoyin ilimi, kimiyya da sauran su; motocin jigilar dalibai hadi da hanyoyin cikin jami’ar.”
“Mun gina hanya mai tsawon 2.5km hadi da magudanan ruwa domin saukin kai komon ma’aikata da daliban jami’a, riyojin burtsatse masu aiki da hasken rana, sanya kayan aiki a ofisoahin ma’aikata da dakunan karatu, sanya kayan aiki a dakunan gwaje-gwajen kimiyya, babban injin bayar da wutar lantarki tare da hada jami’ar da layin wutar lantarki ta kasa don jin dadin ma’aikata da dalibai.” In ji shi.
Har wala yau kuma, Farfesa Haruna ya kara da cewa, ma’aikatar ayyuka da gidaje ta Nijeriya ta gina hanaya a jami’ar mai tsawon mita 300 hadi da gina tangamemen dakin taro na ICT mai daukar mutum 100. Sannan kuma ya ce ita ma ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya ta tona wa jami’ar rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana tare da gina kofifin shiga jami’ar guda biyu. Yayin da ita kuma hukumar sadarwa ta kasa (NITDA) ta gina wa jami’ar cibiyar sadarwa (ICT) tare da sanya na’urorin sadarwa a dakin karatun jami’ar.
Haka zalika kuma ya kara da cewa, a kokarin sa wajen bunkasa aiki, jami’ar ta dauki nauyin tura sama da malamai 122 karo ilimi, a matakin digiri na biyu da na uku, ciki da wajen kasar nan. Baya ga tura karin wasu sama ma’aikata halartar tarukan karo-ilim a Nijeriya da kasashen waje.
Farfesa Andrew Haruna ya bayyana yadda jami’ar ke samun karbuwa da tagomashin daliban da ke shaukin zuwa karatu a FUGA, wanda ta fara da daukar dalibai 800 amma yanzu ta na iya daukar sama da dalibai 1000 a kowace shekara. Ya ce jami’ar ta yaye dalibanta na farko 225 a shekarar 2017/2018 wadanda har sun kammala aikin bautar kasa (NYSC). Wanda a karo na biyu, a 2018/2019 jami’ar ta yaye dalibai 352 wadanda ke shirin tafiyar aikin bautar kasa. Ya ce, wanda yanzu haka muna da jimlar dalibai 577 wadanda su ka kammala karatun digiri a Fuga kuma nan gaba kadan za a gudanar da bikin kammala karatun su.”
A gefe guda, ya bayyana matukar gamsuwarsa da kamun ludayin wadda za ta gaji kujerarsa; Farfesa Maimuna Waziri, saboda cikakkiyar gudumawar da ta bashi wajen aikin gina ci gaban jami’ar tare da kira gareta hadi da manyan jami’an gudanar da jami’ar su bata goyon baya wajen ci gaba daga inda ya tsaya da shan alwashin cewa kofarsa a bude take wajen bata gudumawa don ganin ta samu nasara.
A karshe shugaban jami’ar mai barin gado, ya yaba da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa cikakkiayr damar da ya bashi a matsayin shugaban jami’ar, ministan ma’aikatar ilimi ta Nijeriya, Malam Adamu Adamu da shugaban hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) tare da shugaban hukumar tallafa wa manyan makarantu ta kasa, TetFund bisa karfin gwiwa tare da cikakken hadin kan da suka bashi wajen ganin ya gudanar da jami’ar cikin nasara.

 

Exit mobile version