Connect with us

LABARAI

Fusatattun Masu Haya Da Keke NAPEP Ne Sun Kone Ofishin BIO A Abuja

Published

on

Wasu da ake kyautata zaton masu haya ne da Keke NAPEP, sun kone ofishin Hukumar kula da bin hanyoyi ta shiyyar Abuja, (DRTS), wacce aka fi sani da masu duba lafiyar ababen hawa, (BIO), bakidayan sa.

Makwabta da jami’an hukumar sun ce a cikin tsakiyar daren ranar Alhamis ne aka kone Ofishin, kan kila abin da ake ganin kamar ramuwar gayya ne.

Ofishin wanda ke Unguwar Idu, wacce ke wajen garin na Abuja, kusa da shataletalen, Life Camp, wurin da aka lalata kusan Kekunan na Keke NAPEP 50, a ranar ta Alhamis, a sabili da ‘yar wata fito-na-fito da ma’aikatan hukumar suka yi da masu haya da Keke Napep din, an kone shi ne bakidayansa.

Kwamitin ko-ta-kwana, na hukumar ta birnin tarayyan da kuma masu haya da baburan  na Keke Napep, suna ta dai kai-ruwa-rana ne tun a ranar ta Alhamis, kan ko wadanne hanyoyi ne ya kamata masu Keke Napep din su rika bi a babban birnin tarayyan.

Kwamitin ko-ta-kwanan wanda ke kunshe da ‘yan sanda, jami’an kula da hadurra, jami’an tsaron gidan yari da kuma jami’an na hukumar kula da lafiyan ababen hawa, masu ababen hawa sun jima suna kokawa a kansu.

Majiyar mu ta labarta mana yanda zanga-zangar ta direbobin ta durkusar da kai-komo, a wasu sassan na babban birnin tarayyan. Inda masu Kekunan suka rufe hanya, suka kuma karya wuraren binciken ababen hawa na ‘yan sanda tare da kona tayoyi a sassan Jabi.

Injunan Janareto, Tufafin ma’aikata, Tebura, Kujeri, Kantoci masu dauke da mahimman takardu da bayanai, gami da allunan lambobin ababen hawa, suna cikin abubuwan da jami’an hukumar suka lissafta an kone su.

“Ba za mu iya gane kowa cikin su ba, domin da dare ne suka zo.”

Wani da abin ya faru a kan idonsa ya ce, da misalin karfe 12:30 na dare ne masu Keke napep din suka zo. “Sun zo su da yawa, sai suka yi ta jefa wuta a ofishin, sun kuma katse duk wayoyin lantarkin da yake baiwa ofishin wuta. Wutan ta tashi sosai, ina gidana ina kallon tashin na ta, duk tsawon daren ci take yi.

Ba wani jami’in kungiyar ta masu Keke napep da aka samu wanda zai bayar da bayanin abin da ya faru, sai dai wasu ‘yan kungiyar sun amsa su ne suka kai harin.

“Sun lalata mana Kekunan mu a ranar Alhamis, shi ya sanya masu Kekunan suka kona ofishin na su,” in ji wani mai haya da Keke napep din.

“A kullum sai sun zalunce mu kudade. a kullum muna biyan su Naira 400 na tikitin da su ke ba mu, duk inda kuma suka ganmu sai sun amshi kudi daga gare mu. A jiya kadai sai da suka karbi Naira 12,000 a hannu na. wannan ne ya fusata mu,” in ji wani a cikin su.

Kalu Emetu, Kakakin hukumar, ya tabbatar da kai harin. Ya ce, baya ga Ofishin na su da aka kona, motocin jami’an na, BIO, FRSC, da jami’an hukumar gidan yari, har ma da na Sojoji duk fusatattun sun lalata su.

“Muna ci gaba da gudanar da bincike, ba na son na fadi dukkanin komai don kar ya bata binciken. A yanzun haka ‘yan sanda suna kan lamarin, a karshe muna da tabbacin za su hukunta masu laifin,” in ji Mista Emetu.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: