Fyade Da Hanyoyin Magance Shi Ta Fuskar Nazari

Mene Ne Fyade?

Amsa: To a takaicen takaitawa fyade dai shi ne yin amfani da mace ba tare da izini, yarda, ko son ranta ba; ta hanyar amfani da karfi, ko dubarbaru ko kawar da tunani ko kuma wani abu makamancin hakan. Amma a kula cewar ba mace ce kawai ake yi wa fyade ba, mace ko mata suna iya yi wa namiji fyade, fyade na iya afkuwa tsakanin mace da mace, ko tsakanin namiji da namiji; amma a wannan rubutun bari mu dubi fyade tsakanin jinsin namiji da mace.

Mene Ne Ke Jawo Yawaitar Fyade?

Amsa: Daya daga cikin abubuwan da suke jawo yawaitar fyade sun hada da: Sa kayan banza da wasu mata ke yi, wanda ire-iren wadannan kayan da matan ke sawa a cikin gari suna ratsa unguwanni yana taimakawa kwarai da gaske wajen jawo hankalin wadansu mazajen musamman ashararai, masu shaye-shaye, da kuma wadanda ba sa zama don jiran komai sai don irin wannan damar, wato ‘yan iska, wadanda dama aikinsu ke nan; Mai son zuwa fada ne dama, to bare kuma sarki ya yi kira, ai kawai sai tafiya.

Don haka ire-iren wadancan mutanen da na zaiyano a baya suna samun wata ‘yar dama ko yaya take, sai su yi amfani da ita wajen kiran ire-iren wadancan matan don su shigo wani lungu, ko wani kangon tsohon gini, ko kuma wani gida da ake ginawa wanda ba a karasa ba, idan kuma wadancan matan suka ki bin umurnin wadannan mutanen, to sai su sa karfi don dauko matan don ganin kila wajen da suke irin wannan ta’asar jama’a ba sa kaiwa da komowa a hanyar, daga nan sai su sa karfi su ga cewa sun yi dukkan mai yuwuwa don samun biyan bukatarsu ko ta halin yaya ga wannan baiwar Allah, daga nan sai su kara gaba. Ita kuma su barta cikin wani hali.To kun ga ke nan ya zama irin karin maganar Hausawa da suke cewa “Idan bera na da sata to daddawa ma tana da wari”.

Babu ko shakka lallai shigar da wasu matan suke yi ya baci wajen muni, ya kai makurar kazanta, kuma abun tir da takaici musamman wajen musulmi kuma ‘yan Arewa, wanda ake mana ikirarin kunya. Amma sai ka ga yarinya ta fito daga gidan ubanta kila ma uban ko uwar suna kallonta, babu ko mayafin kirki wato gyale ko kuma hijabi mai girma wanda zai rufe mata jiki. Hasalima za ka iya ganin zanen dan diras dinta, ko kuma za ka iya ganin kalar rigar nonon da ta sa saboda matse mata jiki da kayan da tasa ya yi mata.

Wata ma za ka ga saboda matsewar da kayan ya yi mata da kyar take yin tafiya. Idan kuma babur za ta hau wato dan acaba, sai an yi ta ‘yan dubarbaru tsakaninta da dan acabar, a karshe sai ka ga sai an karkatar da babur din sannan ta samu ta hau, wata ma garin hakan har kayan da tasa yakan yage. To ka ga idan ire-iren wadancan mutanen suka ci karo da irin wadannan matan a wani wurin da babu kowa me kuke tunanin zai faru? Kazalika wani dinkin rigar ma sai ka dauka cewa karamar yarinya ce za ta sa shi, saboda kankantarsa da kuma rashin tsawon rigar, ka ga ana iya ganin cibiya awaje muraratan ke nan.

Wata rigar ma sai ka ga saboda girman hannunta kusan ka iya ganin gefen nonon wanda ta sa rigar a waje. A yayin da wasu kuma saboda girman wuyan rigar kusan kirjinsu da kafadunsu duk a waje yake. Bugu da kari, babu mayafin kirki wai ma fa idan akwai mayafin ke nan. To mai karatu yaya kake gani idan aka yi kacibus da masu fyaden da kuma ire-iren wadannan mata masu shigar banza a wani wuri da babu kowa, ko kuma a wani kangon gini mai kuke jin zai faru? Ke nan sa kaya mai fitar da tsiraici da wasu matan suke yi yana taimakawa gaya wajen yawan aikata fyade.

Saboda Allah sau nawa kuka ji an yi wa masu sa cikakken Hijabi har kasa ko masu shigar kamala fyade? ko da kun ji an yi wa mai sanye da irin wannan hijabin har kasa fyade, to za ku samu an yi wa irin wadancan masu sa kayan banzan babu iyaka, kafin ku ji an yi wa masu sa hijabin guda daya.

Dalili anan shi ne, ko da kin sa matsattsun kaya ko ma dai yaya kayan suke idan aka dauko babban hijabi aka sa to zai zama ya rufe dukkan jiki, ba ma za’a san ko wane kalar kaya kika sa ba, wanda yin hakan shi ne zama lafiyar musulmi a duk inda yake; barin hakan kuwa shi ne rashin zama lafiyarsa ko da ko a ko’ina yake, hakan kuma zai sa ko da masu fyaden sun ga irin wadannan matan masu manyan hijabai a inda ya yuwu su nufesu da fyade din suna ganin iri wannan shigar za su yi shakkar nufosu da wannan niyyar, don ganinsu cikin shigar mutunci, martaba da kuma kamala. Saboda haka nan  ba za su samu karfin gwiwar nufosu da wannan mugun aiki ba.

Guyawun masu aikata fyaden zai yi sanyi, ka ga ke nan ba za su samu karfin gwiwar yin hakan ba, sannan kuma za su yi tunanin idan suka taba ire-iren wadannan mata ba su san abun da zai biyo baya ba, kuma tayuwu abun da zai biyo baya idan suka sake suka taba irin wadannan matan masu sa babban hijabin, ya fi irin na masu wancan shigar banzan tsanani. A nan kun ga ga ladan sa hijabi don rufe tsiraicin jiki, ga kuma kariya daga masu fyade, da ire-irensu, sabanin wadancan masu shigar banzar wanda wata ma ba ka iya gane cewa Musulma ce ko Kirista saboda munin shigar da ta yi.

Kuma ka da mu manta wannan sa kayan mai fitar da tsiraici da wadansu mata suke yi illarsa ba wai ta tsaya ga fyade ne kawai ba, a’a hakan yana yin tasiri kwarai da gaske wajen shigar Iskokai, wato aljanai jikin ire-iren wadannan matan, kamar yadda wani al’jani yake bayani ta yadda suka fi shiga jikin mata. A yayin da wani malami yake kokarin fitar da shi al’janin a jikin matar ta hanyar Rukiyya, al’janin ya ci gaba da cewa “sun shiga jikin wannan mata ne ta hanyar kayan da take yawan sawa mai bayyanar da tsiraicinta kwarai da gaske”.

Dalilin magana akan bayyana tsiraici da wasu daga cikin mata ke yi wanda kuma yin hakan da su ke yi ko alama bai dace da koyarwar Al’kur’ani da sunna ba, shi ne a cikin Al’kur’ani mai tsarki; Allah (S W A) yana cewa a cikin suratul Nur Ayah ta 30-31 ”ka ce wa muminai mata su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu; kuma ka da su bayyana kawarsu face abun da ya bayyana daga gareta; kuma su saka da mayafansu akan wuyoyin rigunanasu ka da su nuna kawarsu face ga mazajensu, ko ubanninsu, ko ubannin-mazajensu, ko ´ya´yansu ko ´ya´yan-mazajensu ko ‘yanuwansu, koya`yan ‘ya’yansu mata, ko matan kugiyarsu, ko abun da hannayensu na dama suka mallaka, ko mabiya wasu masu bukatar mata daga maza, ko jarirai wadan da ba sa tsinkaya akan al’aurar mata.

Haka kuma idan muka koma bangaren malaman tsubbu, Matsafa, Bokaye da ‘yan Bori, su ma suna taka rawar gani wajen kara yawan fyade musamman ga kananan yara daga shekaru biyar zuwa sama, watakila don wani dan siyasa na so ya ci zabe, ko wani dan kasuwa yana so kasuwancinsa ya bunkasa, ko talakan da ke son zama hamshakin mai kudi a dare guda, kawai sai bokansa ya ce mishi sai ya sadu da karamar yarinya sannan zai ci zabe, ko zai samu yalwar kasuwa, ko kuma zai zama katafaren mai arziki. Wasu kuma babu laifin wani boka tsabar jaraba ce kawai da iskanci, da kuma shagalar zuciya, wasu kuwa sun baro iyalansu a can garuruwansu saboda rashin sanin darajar kansu sai su shiga irin wannan mummunar dabi’a ta fyade, yayin da wasu kuwa ‘yan garin ne tsabar rashin aikin yi shi ke sa su shiga irin wannan harkar.

Wasu kuma malamai ne na addinin muslunci ko na boko, a yayin da wasu kuwa tantagayyar jahilai ne kuma babu sana’ar fari balle na baki, sannan kuma za’a iya samunsu a ‘yan garin ko kuma a cikin baki.

Gidajen yada labarai musamman na cikin garin Kaduna da wajenta, kamar DITB/Alheri Rediyo, Freedom Rediyo, FRCN, Inbicta FM, JKD360, Liberty TB/Rediyo, Spider FM, Bision FM, Nagarta Rediyo, da sauran gidajen jaridu irinsu LEADERSHIP A YAU, da sauransu sun sha daukowa da kawo rahotanni akan fyade da ake yi wa kananan yara, ´yan mata har ma da tsofaffi, haka jaridu irinsu Aminiya, Leadership Ayau da Rariya da sauran jaridu da mujallun Hausa da na turanci, duk sun sha kawo tahoto akan matsalar fyade.

A watannin da suka gabata ma a cikin shirin Gari Ya Waye wanda DITB/Alheri Rediyo suke yi kullum safiya, sun kawo wani rahoto mai matukar al´ajabi, tayar da hankali, ban takaici da Allah wadai, akan yadda wata mata ke zargin magidanta da yin lalata da ´ya´yan cikinsa; yarinya ´yar shekara biyar da kuma ´yar shekara takwas. To wai shin sihiri ne ko kuwa tsagwaron sha´awa ce da jarabar tsiya ko kuwa?

Gidajen yada labaran suna kokari gaya wajen kawo rahotanni irin wadannan, da kuma yin tsokaci tare da jin ra´ayin mutane wajen gano hanyar da za a magance ko rage yawaitar fyaden. To ni da nake wannan rubutun a mahangata kuma a nazarce ga hanyar da ya kamata abi domin magance wannan al’amarin na farko ya hada da:

  1. Iyaye su kara sanya ido tare da tsaurarawan gaske akan ire-iren kayan da ‘ya’yansu musamman mata suke sawa. Kuma su kula da mazajen da suke jan ´ya´yansu a jiki musamman kananan yara, sai an yi hattara sosai.
  2. Sarakuna, Hakimai, Dagatai da masu unguwanni su samu kyakkyawan hadin gwiwa a tsakaninsu da shuwagabanin kananan hukumominsu, tun da Ciyaman na karamar hukuma shi ne shugaban tsaro na karamar hukumarsa, sarki kuma shi ne uban kasa gabadaya.

Saboda haka akwai bukatar ya zama ana samun zama a tsakaninsu don tattaunawa na musamman da kuma yin dukkan mai yuwuwa don ganin an magance wanan al’amari na fyade wanda ya addabi al´umma, ta hanyar da ta dace wadda ba zai cutar da wanda harkar ta fyaden ba sana’arsa ba ne.

Har kuma in ya yuwu an kama wani ko wasu da laifin yin fyaden, a gani na babu inda za’a samu hukuncin da ya dace da shi, sai cikin Al’kur’ani mai tsarki, hakan zai taimaka wajen ba wadanda suka mayar da fyaden sana’a tsoro, sai ya zama wasu sun yi wa kawunansu kiyamullaili sun bari tun kafin ayi ram da su. wanan shi ne daya daga cikin nauyin da ya rataya a wuyan shuwagabannin al’umma.

  1. ´Yan majalisun tarayya ko na jiha su yi wa dokar fyade gyaran fuska, ta yadda za ta zama akwai hukunci mai tsanani ga duk mutumin da ya aikata fyade akan karamar yarinya ko babba, hakan zai zamewa wasu izina yayin da suka riska ko suka ji labarin an hukunta wani.
  2. Bangaren shari´a kuma su ji tsoron Allah wajen gudanar da adalci yayin shari´ar da ta shafi fyade, saboda a halin yanzu rashin wanzar da adalci wajen shari´a shi yake sanyaya gwiyawun iyayen wadanda aka yi wa ´ya´yansu fyade sai dai su yi Allah Ya isa, wata shari´a sai a lahira.
  3. Hukumomi da kungiyoyi su ci gaba da jajircewa da gwagwarmaya wajen ganin sun kwatowa wacce aka yi wa fyade hakkinta; kungiyoyi da dama jama’a sun shaida da kokarinsu da jajircewarsu wajen bi wa wadanda aka zalunta hakkinsu.
  4. Kungiyoyi da hukumomin gwamnati wadanda alhakin abun ya shafa, su dinga shirya wani taro akai-akai don wayarwa iyaye da kai akan yadda za su kare ´ya´yansu daga sharrin masu fyade da kuma yadda iyaye za su iya gane yarinyar da aka yi wa fyade, da matakin da za su dauka.
  5. Ga iyaye da sauran al’ummar gari kuma, ya kamata wasu masu irin mummunar akidar nan na idan ba su suka haifi yaro ba, ba za su tsawata musu akan wani abu da suke yi maras kyau ba. Ya kamata su bar wannan mugun halin na nuna bambanci a tsakanin yara. Masu iya magana kan ce ”Da na kowa ne, mugu kuwa sai mai shi” su ci gaba da tsawatawa yara tare da yi musu nasiha tare da kuma sanya ido a duk inda suke, wuraren zuwansu, mu´amalarsu da inda suke shiga lungu- lungu kwararo-kwararo duk wurin da suka ga ba su amince da wurin ba to su garzaya su kai rahoto ga masu unguwanni, Dagatai ko Hakimai, su kuma su kai zuwa inda ya dace don daukar matakin da ya dace cikin hanzari.

Allah Ya sa mu fi karfin zukatanmu, Allah Ya tseratar da mu daga aikata masha´a, Ya kuma ba mu ikon aikata daidai, Ya kuma sa mu akan hanya madaidaciya.

Ma’assalam!

Exit mobile version