Connect with us

LABARAI

Fyade: Gbajabiamila Ya Jinjina Wa Kakakin Bauchi Kan Dakile Cin Zarafin Bil’adama

Published

on

Shugaban Majalisar wakilai ta tarayya, Honorabul Femi Gbajbiamila, ya jinjina tare da yaba wa Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Hon. Abubakar Y. Suleiman bisa gabatar da kudurin da zai kai ga shawo kan matsalar cin zarafin al’umma a jihar Bauchi.
Yayi yabon ne a ranar Talata a yayin wata ganawa da shugaban yayi da shugabanin majalisar Bauchi, Ekiti, Edo da kuma jihar Filato hadi da wasu, kamar yanda wata kwafin sanarwar da Abdul Ahmad Burra, mai magana da yawun Kakakin majalisar Bauchi ta shaida.
Sanarwar ta kara da cewa, ganawar ta gudana ne ta kafar sadarwa ta ‘Zoom’ biyo bayan wani alkawarin da Kakakin yayi makonni biyu da suka gabata a lokacin da ke ganawa da wasu kungiyoyin fararen hula kan lamarin nan da take neman zama ruwan dare na cin zarafin mata, fyade da keta haddin mata da yara kanana hadi da al’umma a cikin kasar nan.
Kakakin majalisar tarayyar Gbajabiamila wanda ke nuna jin dadinsa bisa himmar da Kakakin majalisar Bauchi ya ke yi kan batun fyade da sauran cin zarafin jama’a, inda ya nemi sauran shugabanin majalisar jihohin kasar nan da su maida hankali kan dokar kare hakkin yara da tauye wa al’umma hakki.
A jawabinsa na godiya bisa wannan yabon, Kakakin majalisar Bauchi, Abubakar Y. Suleiman, ya shaida cewar ya dauki nauyin gabatar da kuduri na musamman da zai kai ga dakile matsalar cin zarafin al’umma ne a sakamakon yawaitar kesa-kesan fyade, ‘yan bangar siyasa, da sauran kalubalen cin zarafin jama’a a jihar Bauchi da ma kasa baki daya.
A cewar shi, abokan aikinsa ‘yan majalisar jihar masu daraja cikin kankanin lokaci suka amince da kudurin inda ya ke mai shaida cewar yanzu haka ana kan matakin jin ra’ayoyin jama’a a kansa bayan da kudurin ya wuce karatu na farko zuwa na biyu a kwaryar majalisar ba tare da wani suka ko kin amincewa da shi ba.
Ganawar ta kai ga cimma matsayar cewa Kakakin majalisar Bauchi wanda kuma shine shugaban taron ganawar shugabanin majalisar shiyyar arewa maso gabas da ya maida hankali wajen jawo hankalin sauran shugabanin majalisar da su yi koyi da sa’ayinsa kan irin wannan kudurin da zai kai ga rage cin zarafin al’umma.
Da ya ke magana kan shugabantar taron ganawar da aka daura masa, Honorabul Abubakar Sulaiman ya sha alwashin tuntubar sauran takwarorinsa da su ke shiyyar arewa maso gabas don cimma manufar da aka sanya a gaba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: