Khalid Idris Doya" />

Fyade: Gwamnatin Ogun Ta Dakatar Da Kwamishina Bisa Zargin Keta Haddin ’Yar Shekara 16

Gwamnatin Jihar Ogun ta dakatar da Kwamishinan Muhalli na jihar, Mista Abiodun Abudu-Balogun, bisa zargin yi wa karamar yarinya fyade.

An dakatar da Mista Abudu-Balogun ne dai daga ofis bisa zargin cin zarafi da keta haddin wata yarinya ‘yar shekara 16 mai suna Barakat Mayowa Melojuekun.
A sanarwar manema labarai da sakataren gwamnatin jihar, Tokunbo Talabi, ya fitar a ranar Lahadi a Abeokuta, ya sanar da dakatar da gwamantin ta yi wa Kwamishinan har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zargin da ake masa.
Ya yi bayanin cewa, gwamnatin jihar ta dauki matakin dakatar da Abudu-Balugun ne domin ba shi cikakken damar samun lokacin bayyana domin amsa tambayoyin da ‘yan sanda ke masa kan zargin da ke kansa.
Sanarwar ta shaida cewar, gwamnatin jihar ko da wasa ba za ta lamunci cin zarafin bil-adama ba, yana mai cewa idan har aka tabbatar da kwamishinan ya aikata wannan laifin, to tabbas gwamnati za ta nuna masa fushinta, in kuma bincike ya wankesa a shirye gwamnatin take ta sake rungumarsa da tsarkakken niyya.
Talabi ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta yi dukkanin mai yiyuwa domin tabbatar da adalci ya wanzu a tsakanin wannan kes din tare da samar wa mai gaskiya da gaskiyarsa da hukunta mai laifi in an samu.
Sanarwar ta ce, gwamnatin ta umarci dakataccen kwamishinan da ya mika ragamar mulkin ma’aikatar a hannun babban sakataren dindindin na ma’aikatar muhalli ta jihar nan take.

Exit mobile version