Nasir S Gwangwazo" />

Fyade: Rundunar ’Yan Sandan Kano Ta Tsefe Bayanai

 

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano a karkashin jagorancin Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, CP Habu A. Sani, ta hattama wani rahoto na musamman, wanda ya tsefe bayanai kan yadda al’amarin fyade ya ke kasancewa a fadin jihar.

Bayanin hakan ya zo ne a wata tattaunawa ta musamman da CP Sani ya yi da LEADERSHIP A YAU cikin makon mai shudewa, inda ya yi bayani dalla-dalla kan irin bayanan da su ka tattaro, don kawo karshen wannan dabi’a da ta addabi al’umma a yankin arewacin Nijeriya ta yi wa mata da kananan yara fyade.

“Mun bi diddigi mun hada kundin rahoton bayanai na musamman kan aikata laifin fyade tun daga kan wadanda a ke yi wa zuwa masu aikatawar da yanayin da a ke yi da kuma guraren da a ke aikatawa, domin samar da bayanan da za su taimaka wa jama’a dauykar matakan dakile aikata masha’ar da mu kanmu,” in ji kwamishinan.

Rahoton, wanda a ka samar da bayanai na watanni shida daga 1 ga Janairu zuwa 30 ga Yuni, 2020, ya nuna cewa, an kama mutane 50 bisa zargin aikata wannan mummunar dabi’a, inda kuma bakidayansu a ka gurfanar da su a gaban kotu, yayin da a ka samu nasarar hukunta 27 daga cikinsu.

Binciken rundunar ’yan sandan ya  nuna cewa, a ranakun Litinin a ka fi samun masu aikata laifin da kashi 28.9, inda Alhamis ke bi ma ta da kashi 26.7, sai kuma Lahadi mai kashi 24.4. Sauran ranakun su ne Talata da ke can nesa da kashi 8.9, sannan Juma’a mai kashi 6.7, yayin da Laraba ke da kashi 4.4 cikin 100.

Amma abin mamaki shi ne, ba a taba samun aikata fyade a ranar Asabar ba, duk tsawon wannan lokaci.

Idan a ka lura, an fi samun aikata wannan laifi a ranakun aiki da kuma wadanda iyaye maza ke shagala da wasu al’amura na rayuwa. Misali; Litinin kusan kowa ya na fita aiki, Alhamis ce da ke kusa da Juma’a, wacce rana ce da a ka fi mayar da hankali ga ibada. Saboda haka zai iya yiwuwa a na cin kasuwar fyaden ne a Alhamis kafin Juma’ar. Lahadi kuwa watakila iyaye maza kan fi shagala wajen aiwatar da wasu al’amura wadanda su ka shafe su, kamar ziyara da kananan ayyuka, amma su kan fi yin zaman dirshan a gida, su kuma sanya ido kan iyalinsu.

“Mu na nan mu nan bincike wajen tabbatar da dalilan da su ka sanya a ka samu wadannan rabe-rabe a hukumance,” in ji CP Habu.

Ya kuma yi bayani kan yadda lamarin ke da alaka da hannun da ke rikon yaran da a ka fi yi wa fyade.

“Kashi 60 cikin 100 a yaran da a ke yi wa fyade su na hannun iyayensu ne. Wato auren iyayensu, uwa da uba, bai rabu ba. Kashi 17.8 kuma a hannun uwa kadai su ke rike, inda kuma kashi 11.1 kakarsu ce ke rike da su,” a cewar Habu, wanda ya kara da cewa, “kashi 8.9 kuma a hannun dangi a ke rike su, sannan kashi 2.2 su ke rike a hannun uba bayan rabuwarsu da uwar.”

Kan hakan CP Habu ya yi karin haske da cewa, “idan ka lura a nan, duk da cewa, an samu kaso mafi yawa na kashi 60 su na tare da iyayensu ne, amma maza su kan dauke kai, su sake, su sakar wa iyaye mata nauyin kula da sa ido kan ’ya’ya. Don haka ne ma ka ga kashi mafi yawa na biye da wannan shi ne na ’ya’yan da uwarsu ce ke rike da su, wato 17.8, kuma za ka ga mai bi ma sa shi ne, rikon kaka, wato kashi 11.1, amma mafi karanci shi ne na 2.2, wadanda uba ne kadai ya ke rike da ’yarsa, saboda watakila ya kan fi maida kai wajen sa ido kan ’ya’yan a irin wannan yanayi. Amma dai karfafa bincike ne zai kara tabbatar ma na da ko wane ainihin dalili ne.”

Binciken rundunar kuma ya kara cewa, kashi 22.2 na fyade ya afku ne a watan Janairu, yayin da kashi 17.8 a Fabrairu, ya sauka zuwa kashi 13.3 a Maris. Watan Afrilu kuma ya karu zuwa kashi 15.6, sai ya koma kashi 13.3 a Mayu, amma an sake samun hauhawar fyaden zuwa 17.8 a Yuni.

Bayanan sun kara da cewa, kashi 58.3 na wadanda a ka yi wa fyade shekarunsu ya fara daga shida zuwa 12 ne, yayin da masu shekara 13 zuwa 17 ke da kashi 25. Jarirai zuwa ’yan shekara biyar ne ke da biye da kashi 8.3, inda ’yan shakara 18 zuwa sama su ka kasance mafi karanci da kashi 4.2 na wadanda a ka yi wa fyade.

CP Habu ya kuma shaida wa LEADERSHIP A YAU irin mutanen da su ka fi kamata a yi kaffa-kaffa da su daga cikin masu aikata fyade, ya na mai cewa, wadanda su ka fi aikata su ne matasa masu shekaru 18 zuwa 25 a duniya, domin su ne bincike ya ba su kashi 32 na yawan masu aikata fyade a jihar.

Ya kara da cewa, masu bi mu su kwa su ne ’yan shekara 26 zuwa 40, wadanda su ke da kashi 24 cikin 100, inda kuma ’yan shekara 40 zuwa sama su ke da kashi 12. Mafi karancin masu aikata fyaden kuwa su ne, kananan yara zuwa lokacin da su ka cika shekara 18, domin su ne su ke da kashi takwas kadai.

Abin mamaki da rahoton shi ne, mafi karancin masu aikata fyade su ne zawarawa maza, domin binciken ya nuna cewa, kashi hudu cikin 100 daga masu aikata laifin ne kawai zawarawa, inda wadanda ba su taba sanin dadin rayuwar aure ba su ke da kaso mafi tsoka na kashi 72 cikin 100. Don haka da su ne iyaye ya fi kamata su fi yin kaffa-kaffa da ’ya’yansu a kansu. Binciken ya kuma nuna cewa, masu aure su ne su ke da kashi 24 na masu aikata wannan masha’a.

Wani karin ban mamaki shi ne, bayanan sun ce, kashi 16 ne kacal na masu aikata shaye-shaye a jihar ta Kano su ke aikata fyade, yayin da sauran kashi 84 cikin 100 su ke aikata shi a cikin hankalinsu tangararan ba tare da bugun maye ba.

CP Habu Sani ya kara shaida wa LEADERSHIP A YAU cewa, lallai ya wajaba ga iyayen yara su rika matukar sa ido kan zirga-zirgar ’ya’yansu da tsakar rana zuwa yamma, domin a wadannan lokuta ne masu aikata wannan ta’annati na fyade su ka yin bushasharsu, domin kashi 48.9 na fyaden da a ka aikata a jihar an yi ne daga misalin karfe 12:00 na rana zuwa 6:00 na yamma.

Kwamishinan ya kara da cewa, akwai kuma masu yin sammakon duku-dukun safe misalin karfe 6:00 na safe zuwa 12:00 na rana da ke da kashi 31.1. Don haka dole a sa ido kan wannan lokaci ma.

A cewarsa, lokacin da ke biye da wannan wajen aikata fyaden shi ne, tazarar karfe 6:00 na yamma zuwa 12:00 na dare, inda lokacin ke da kashi 17.8. Amma rahoton ya ce, daga 12:00 na tsakar dare zuwa 6:00 na safe iyaye za su iya sharara barcinsu, amma da ido daya, domin akwai kashi 2.2 da a ka samu da irin wannan ta’annati ya afku a wannan lokaci.

CP Habu ya yi karin haske da cewa, yanayin lokacin da a ka fi aikata fyade daga 12:00 na rana zuwa 6:00 na yamma ya na kuma jaddada cewa, daga dukkan alamu an fi samun aikata fyade a lokacin ’ya’ya ke karkashin kulawar iyayensu mata, domin a irin wannan lokacin iyaye maza sun bazama nema, sun bar iyaye mata da kula da ’ya’yan.

Da rahoton ya tabo batun guraren da a ka fi aikata ta’annatin fyade kuwa, ya ce, kangayen gine-gine ne guraren da a ka fi yin wannan masha’a, domin kashi 33.3 na wadanda a ka cafke, an kama su ne a kangaye. Mai bi wa kango kuwa su ne, gonaki, wadanda kashi 20.8 na laifin a ke aikatawa a ciki.

Ya kuma kara da cewa, lallai ne a kula da guraren wadanda ’ya’ya ke zuwa, domin kashi 16.7 na wadanda a ka yi wa fyade an yi mu su ne a gidajen masu aikata laifin. Abin nufi a nan shi ne, ’ya’yan ne su ke kai kansu. Sai dai kuma ya ce, shaguna ma su na taka muhimmiyar rawa wajen tafka ta’asar fyade, domin kashi 14.6 a na yi ne a cikinsu.

Daga nan sai ya nuna cewa, duk da haka akwai gurguzun masu aikata wannan laifi kashi 10.4 da ke iya nukar gari su shiga har gidajen yaran su aikata fyade nesa fiye da yadda masu aikatawa a kasuwanni da makarantu, wadanda ba su wuce kashi 2.1.

Batun hanyoyin da masu laifin ke bi wajen jan hankalin yaren da su ke yi wa fyaden kuwa, CP Habu ya ce, kashi 44.4 daga cikinsu a na jan ra’ayinsu da kudi ko wani abinda a ke ci ne (kamar biskit ko alewa da sauransu), yayin da kuma kashi 17.8 na makota da ’yan dangi ke amfani da alakarsu wajen ribar yaran.

Samarinsu da masu amfani da dama lokacin shagalin bikin aure da kuma masu amfani da karfin tsiya ko wata barazana a gidajen iyayen yaran sun kai kashi 6.7, yayin da yara masu tabin hankali da wadanda a ka bari a gida su kadai da kuma malamansu na makaranta su ke lalata su da kashi 2.2. Sauran kuma, wadanda ba a tantance su ba, sun kai kashi 8.9.

Rahoton ya kuma gano cewa, kashi 24 na masu aikata fyade sun ce su na yi ne sakamakon rashin aure, inda kashi 76 kuma ba su bayyana dalilansu ba.

Bugu da kari, yaran da ba su wuce samun ilimin makarantar firamare ba sun fi gamuwa da wannan iftila’i na fyade, inda kashi su ka kai kashi 35.6, sai kuma wadanda sam ba su halartar kowacce makaranta sun kai kashi 33.3, inda kuma kashi 17.8 su ka kasance masu zuwa makarantar islamiyya. Masu ilimin sakandare ne mafi karanci da kashi 13.3 a cikin wadanda a ke yi wa fyade a Jihar Kano.

Ta fuskar tattalin arziki kuwa, ’ya’yan ’yan kasuwa sun fi fuskantar barazanar fyade, domin kashi 26.7 na wadanda a ka yi wa fyade iyayensu ko marikansu ’yan kasuwa ne, kamar yadda bincike ya nuna. Haka nan, kashi 24.4 kuwa iyayensu leburori ne, yayin da kashi 22.2 iyayensu su ka kasance direbobi, sannan’ya’yan manoma su ka ja kashi 17.8 cikin 100, sai kuma ’ya’yan ma’aikatan gwamnati ke da mafi karanci na kashi 8.9.

Abin la’akari a nan shi ne, iyayen wadannan yara ba a san su da yin zurfin ilimin addini ko na zamani ba. Haka zalika, iyayen nasu su na fama da talauci bisa la’akari da yanayin sana’o’insu da kuma cewa, kudi ko abin ci ne hanyar da a ka fi amfani da su wajen jan ra’ayin yara, don yi mu su fyade.

CP Sani ya yi kira ga iyaye da masu rike da ’ya’ya da su yi la’akari da bayanan da a ka bayar, domin taimaka wa rundunar wajen kubutar da ’ya’yansu daga wannan mummunan yanayi, ya na mai cewa, da zarar an ga wani motsin da ba a yarda da shi a irin wadannan gurare da yanayi da a ka zayyana, to a ankarar da rundunar tare da daukar matakin da ya dace cikin gaggawa, don gujewa afka wa danasani.

Ya kara da cewa, rundunarsa ta shirya tsaf wajen ganin an kawo karshen aikata wannan ta’annati na fyade a fadin jihar bakidaya.

Jihar Kano dai ita ce jiha mafi yawan al’umma a Nijeriya da Afrika kuma akalla mafi yawan hada-hadar kasuwanci, tattalin arziki, noma, sufuri da siyasa a Arewacin Nijeriya. Don haka rahoton zai iya yin aiki a yankin bakidaya

Exit mobile version