Fyade Ya Yi Sanadin Kisan Kai A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira

Fyade

Daga Muhammad Maitela,

Wata ‘yar gudun hijira a jihar Borno, mai suna A’isha Umar, ta kashe kanta ta hanyar daba wa cikinta wuka, bayan fyade da wani jami’in kungiyar ayyukan jinkai ta kasa da kasa ya yi mata.

Bugu da kari, an garzaya da marigayiyar a dakin bai wa maras lafiya kuta ta gaggawa a Asibitin Koyarwa Ta Jami’ar Maiduguri, bayan da aka zargi jami’in da aikata mummunan alkaba’i ga malama A’isha, a gidansa da ke Rukunin Gidajen 303 (Housing Estate), da ke kusa da sansanin yan gudun hijira na ‘Darori IDP camp’, a birnin Maiduguri, bayan ya yaudari marigayiyar da cewa ta share masa daki.

Bayanai sun ce mutumin da ake zargin sunan shi Huzaif Adam, dan kimanin shekara 35 a duniya, wanda rahotanni a jihar su ka tabbatar da cewa ya yi amfani da karfin tuwo wajen aikata alfasha (fyade) da baiwar Allah, a lokacin da ta shiga dakinsa. A hannu guda kuma, wata majiyar da ke makobtaka da inda abin ya faru ta bayyana cewa, Aisha Umar ta yi ta ihun neman taimakon makobtansu a lokacin da Adam yake kokarin yi mata fyaden, amma ina, kan kafin a kawo mata dauki ya riga ya aikata masha’ar da ta lalata rayuwarta.

Makobtan sun shaida yadda suka balle kofar da nufin kai wa marigayiyar dauki, wanda daga bisani Aisha ta fito a gigice zuwa dakin da Adam ke dafa abinci inda ta zari wuka ta daba wa cikinta. Wanda nan take aka garzaya da ita Asibiti.

Wani jami’in yan-sanda a Maiduguri da yake tabbatar wa da wakilinmu faruwar lamarin, ya ce an kulle wanda ake zargin zuwa ofishin yan-sandan yanki da ke unguwar Gwange bayan kama shi wanda kuma daga bisani aka mika shi ofishin yan[1]sanda binciken manyan laifuka (SCID). Jami’in ya kara da cewa, “Mun kama wanda ake zargi da aikata laifin, sannan kuma yanzu haka an mika shi a ofishin yan-sandan binciken manyan laifuka.” Ya bayyana.

A nata bangaren, Babbar Daraktar Kungiyar ‘New Nigeria and Youth Empowerment Initiatibe’, Comrade Lucy D. Yunana, ta bayyana cewa bayan da ta samu labarin faruwar al’amarin, ta garzaya wadannan wurare guda biyu; ofishin yan[1]sandan Gwange da Asibitin Koyarwar Jami’ar Maiduguri, domin gani da idonta kan yadda abin ya faru. “An yi magana dani kai tsaye a ofishin mu kuma daga bisani na yi magana da Kwamishinan Wasanni dangane da abin da ya faru.

Sannan kuma abin ya faru ne kusa da inda muke- Yankin 303/202 EFCC. Na ga wanda ake zargin da idona kuma na zanta dashi, kana kuma na ga gawar yarinyar da al’amarin ya faru da ita a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH). Gaskiya wannan abin bakin-ciki ne wanda ko shakka babu ya dace ayi wa wannan baiwar Allah adalci.”

“Yarinyar nan sai faman kukan neman agaji take, ta na gaya masa cewa: ‘Me yasa za ka yi min haka?’ Maimakon sanya kunya a idon mahaifana, bayan kyakkywar tarbiyar da suka bani, gara na mutu da na je musu da wannan mummunan labari a gida.” Ta bayyana a cikin alhini.

Exit mobile version