Connect with us

LABARAI

Fyade: Yara A Gombe Sun Bukaci Aiwatar Da Dokar Kare Hakkin Yara

Published

on

Yara a jihar Gombe sun yi kira ga gwamnatocin jiha da ta tarayya da su maida hankali tare da fitar da tsare-tsaren kula da yara kan cutar Korona.

Sannan, yaran sun kuma yi kira da babban murya ga gwamnatoci na a tabbatar da amincewa da dokar kare hakkin yara domin karesu daga cin zarafi kama daga fyade da sauran munanan ayyuka na keta musu haddi a cikin al’umma.
Majalisar yara ta jihar Gombe ne ta yi wannan kiran a budaddiyar wasikar da su suka aike wa shugaban kasa Muhammadu Buhari gami da gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya domin raya bikin ranar yaran Afirka.
Yaran da su ke kiran da a jawo yara a jika gami da musu adalci, sun yi bayanin cewa yara a Gombe da ma kasa baki daya suna tsananin fuskantar cin zarafi kama daga fyade, tashin hankali, firgici da zama cikin rashin aminci a kowani lokaci.
Yaran sun bukaci a samar da kotun yara ta musamman da za take tabbatar da tursasa a bin doka a kuma sanya bangaren ‘yan sanda, jami’an tsaro gami da soji domin tabbatar da aiwatar da cikakken dokar kare hakkin yara Child Rights Act (CRA).
A wasikar da Kakakin majalisar yara na jihar Gombe Hon. Umar Faruk ya karanto a gaban kwamishinan kula da harkokin mata da bunkasa jin dadin al’umma, Mrs Naomi Awak, ya shaida cewar suna bukatar gwamnati ta samar da tsarin na musamman da zai kai ga bunkasar rayuwar yara.
A daidai lokacin da yaran ke yaba wa kokarin gwamnatoci a dukkanin matakan bisa daukar kwararan matakan dakile cutar nan ta Korona, sun kuma nuna damuwarsu bisa yadda aka wofintar da yara kanana musamman a yankunan karkara ba tare da nusar da su matakan kariya daga wannan cutar ba, sun nemi gwamnati ta sauya gami da fitar da tsarin da yara za su ankare daga cutar.
Da ta ke jawabi bayan amsar wasikar da aka ba ta don ta mika wa gwamnan jihar Gombe, Mrs Naomi Awak, ta bada tabbacin jihar na sauraron koken yara, tana mai shaida cewar gwamnatin jihar ta himmatu wajen kyautata rayuwar yara da ma ta bayyana cewar yara ‘suna cikin ran gwamnatin’, ta kuma shaida cewar akwai tsare-tsaren kara wayar da kan yara a bangaren ilimi da suke kai.
Ta kuma shaida cewar gwamantin ta kan aiki wajen ganin dokar kare hakkin yara CRA ya fara aiki a jihar.
Ta shaida cewar nan ba da jimawa ba gwamnan jihar Inuwa Yahaya zai yi wani abu kan wannan dokar kare hakkin yaran.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: