Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home DAGA BIRNIN SIN

Ga Dalilan Da Suka Sa Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Samu Farfadowa Da Bunkasuwa

by Sulaiman Ibrahim
March 16, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
3 min read
Ga Dalilan Da Suka Sa Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Samu Farfadowa Da Bunkasuwa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga CRI Hausa

Tun bayan da kasar Sin ta samu farfadowar tattalin arziki a shekarar 2020, batun ko za ta ci gaba da raya tattalin arzikinta a shekarar 2021 kamar yadda ake fata, yana ci gaba da janyo hankulan kasashen duniya. Bayanin da gwamnatin kasar Sin ta fidda, na nuna cewa, a cikin watannin Janairu da Fabrairu na bana, bukatun al’umma na ci gaba da karuwa, ana kuma samar da guraben aikin yi da daidaita farashin kayayyaki, baya ga yadda kasuwanni ke farfadowa yadda ya kamata. Lamarin da ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin, na ci gaba da farfadowa da karuwa bayan rubu’i na biyu na shekarar 2020.
Bayanin na nuna cewa, idan aka magance tasirin da barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta haifarwa tattalin arzikin kasar Sin, saurin karuwar harkokin masana’antu tsakanin watannin Janairu da Fabrairu cikin shekaru biyu, ya kai kashi 8.1 bisa dari, kuma adadin ya kai kashi 6.8 bisa dari na harkokin ba da hidima, sa’an nan, adadin ya kai kashi 1.7 bisa dari na fannin kadarori, da kuma kashi 3.2 bisa dari a fannin kayayyakin yau da kullum da ake sayarwa. Lamarin da ya nuna cewa, manyan alkaluman tattalin arzikin kasar Sin, suna karuwa yadda ya kamata.
Ci gaban farfadowar tattalin arzikin kasar Sin yana nuna cewa, tattalin arzikin kasar zai ci gaba da bunkasuwa cikin dogon lokaci dake tafe, a sa’i daya kuma, ya nuna cewa, matakan da kasar Sin ta dauka daga rubu’i na biyu na shekarar 2020 zuwa yanzu, domin dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, na tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki, suna ci gaba da taka rawa yadda ya kamata.
Ko da yake a bana, cutar numfashi ta COVID-19 ta sake barkewa a wasu sassan kasar Sin, amma, duk da haka, an tabbatar da farfadowar tattalin arziki bisa matakan dakile yaduwar annoba da gwamnatin kasar ta dauka, da kuma manufofin raya tattalin arziki da aka fito da su. Kamar manufar yin kira ga ’yan kasar, da su yi bikin bazara a wuraren da suke aiki, ba kawai matakin ya ba da gudummawar dakile yaduwar annoba, ya kuma ba da taimako wajen raya harkokin masana’antu.
A sa’i daya kuma, kyautatuwar yanayin kasashen duniya, shi ma ya taimaka wajen bunkasuwar tattalin arzikin Sin. Bayan da aka fara yi wa al’ummomin kasa da kasa alluran rigakafin cutar COVID-19, harkokin masana’antu a wasu kasashe sun fara samun farfadowa, lamarin da ya sa, adadin fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare ya karu a kasar Sin. Daga watan Janairu zuwa na Fabrairu na bana, adadin kayayyakin da kasar Sin ta fitar zuwa kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN ya karu da kashi 40 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar bara. Kana, adadin kayayyakin da kasar Sin ta fitar zuwa kasar Amurka ya karu da kashi 70 bisa dari, idan aka kwatatan da na makamancin lokacin shekarar bara. A sa’i daya kuma, farfadowar tattalin arzikin kasar Sin, ta taimakawa kasashen duniya wajen raya tattalin arzikinsu.
Wani abu mai muhimmanci shi ne, harkokin kirkire-kirkire na ci gaba da bunkasa kamar yadda ake fata. Adadin bunkasuwar fasahohi na zamani tsakanin watan Janairu da watan Fabrairu cikin shekaru biyu, ya kai kashi 13 bisa dari, kuma adadin ya kai kashi 10.2 bisa dari a fannin sarrafa na’urori. Baya ga haka kuma, fannin samar da sabbin na’urori, yana ci gaba da samun bunkasuwa, kamar motoci masu amfani da wutar lantarki, da mutum-mutumin inji da ake amfani da su a masana’antu da sauransu. Ana iya cewa, tattalin arzikin kasar Sin na samun bunkasuwa mai inganci.
A yayin taruka biyu na bana, gwamnatin kasar Sin ta jaddada cewa, za ta ci gaba da aiwatar da manufofin raya tattalin arziki da ta tsara a baya, domin taimakawa kamfanonin kasar da kuma tabbatar da dauwamammen ci gaban tattalin arzikin kasa. Lamarin da ya sa kaimi ga kamfanonin kasar wajen neman ci gaba.
Kasar Sin tana fatan tattalin arzikinta zai karu fiye da kashi 6 bisa dari a bana. Da yake tsokaci kan batun, shugaban kula da harkokin Sin da arewa masu gabashin yankin Asiya na kamfanin Euroasia Michael Hirson ya ce, wannan ba wani buri ne mai wahala ba ga kasar Sin, inda ya nuna aniyar kasar Sin wajen neman bunkasuwar tattalin arziki mai inganci, a maimakon saurin kasuwar tattalin arziki da bai dace ba, Sin ta tsai da wani kuduri ne daidai. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

SendShareTweetShare
Previous Post

Kasar Sin Ta Yi Hangen Nesa Wajen Tunawa Da Jami’an Wanzar Da Zaman Lafiya Yayin Da Take Bada Gudunmuwar Rigakafi

Next Post

Gungun Bangarori Hudu Ba Zai Cimma Nasarar Adawa Da Sin Ba

RelatedPosts

Ci Gaban Kasar Sin A Fannin Fasaha Ba Ya Tsoron Danniyar Amurka

Ci Gaban Kasar Sin A Fannin Fasaha Ba Ya Tsoron Danniyar Amurka

by Sulaiman Ibrahim
18 hours ago
0

Daga Bilkisu Xin A ranar 8 ga wata, ma’aikatar kasuwanci...

Takunkuman Amurka Da Birtaniya Kan Sin Sun Keta Dokokin Kasa Da Kasa

Takunkuman Amurka Da Birtaniya Kan Sin Sun Keta Dokokin Kasa Da Kasa

by Sulaiman Ibrahim
18 hours ago
0

Daga CRI Hausa Tsohon Jakadan Italiya a kasar Sin, Alberto...

Masanan Sin Da Afirka Suna Fatan Za A Kara Yin Mu’amalar Al’adu Da Juna

Masanan Sin Da Afirka Suna Fatan Za A Kara Yin Mu’amalar Al’adu Da Juna

by Sulaiman Ibrahim
18 hours ago
0

Daga CRI Hausa Kwalajin nazarin harkokin Afirka na kasar Sin,...

Next Post
Gungun Bangarori Hudu Ba Zai Cimma Nasarar Adawa Da Sin Ba

Gungun Bangarori Hudu Ba Zai Cimma Nasarar Adawa Da Sin Ba

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version