Abdulrahman Aliyu" />

Ga Wuta Ga Masara: Kalubalen Da Matasa Ke Fuskanta A Makarantun Gaba Da Sakandire

Shirin Shiga Ruwa Tun A Tudu Ake Fara Shi

Kulin kulifit abu dunkule,

Kalau na kale kalubale,

Kacinci ka-ci, miye abin,

Da ke yado, kuma dunkule?

(Wakar Kalubale ta Akilu Aliyu)

Kalmar kalubale, kalma biyu ce masu ma’ana daban-daban a harshen Larabci, aka aro su kuma aka dunkule su wuri guda cikin harshen Hausa da ma’ana guda. Wato kalu, mai ma’anar suka ce, da kuma bale, mai ma’anar Eeh, a cikin Larabci. Sai harshen Hausa ya aro su kuma ya dunkule su wuri guda da ma’ana daya, wato kule ko tara (Newman 1997:39), misali inda ake cewa yaro ya tari abokin wasansa, wato yaro ya gayyaci abokin wasansa, Ko kuma wurin da yara kan ce: idan na ce kule ka ce cas, wato idan na gayyace ka, ka amsa.

Kenan, kalubale wani tudu ne da sai an tsallaka a yayin da aka dumfari isar da wata manufa a kokarin cim ma wani mataki ko kai wa ga wani bagire da aka tunkara a rayuwa. Idan kuwa haka ne, kuma hakan ne, rayuwar dan’adam gaba-dayanta damfare take da kalubale a kowane mataki.

Don haka, ya dace a fara waiwayen baya, domin idan ana batun rayuwar matasa a makarantun gaba da sakandire, hakika kallon rayuwar sakandiren, kila ma har da ta firamare zai kara mana hasken musabbabin kalubalen da matasan ke fuskanta a makarantun gaba da sakandire.

Shekaru 115 kenan da ilimin boko ya sami gindin zama a arewacin Nijeriya (wato daga shekarar 1903 zuwa 2018), amma har yanzu bai sami irin tagomashin da ya dace ya samu ba, idan an kwatanta da kudancin kasar. Abin da za a iya cewa ya sauya shi ne yawan wadanda suka rungumi neman ilimin na boko amma har yanzu yana fama da masassara ta rikon sakainar kashi. Shi ya sa ba a damu da wane irin fandishan za a yi wa yaro ba tun daga karatun firamare zuwa sakandire domin shirin shiga fagen daga a matakin gaba da sakandire. Matsaloli da suka jibinci dabaru da tsarin koyarwa da kayan aiki musamman a makarantun gwamnati su ne kan gaba wajen aza tubalin kalubalen ilimin boko a matakan farko. Har ila yau, rashin bibiya daga iyaye ya taimaka gaya wajen baro shiri tun rani. Duk da cewa akwai matsi na tattalin arziki, amma galibi wasu iyayen sukan fake da talauci wajen kin ba ilimin ‘ya’yansu muhimmanci a matakin farko . Ire-iren wadannan matsaloli da wasu da ba a ambata ba, su ne suke gina tunanin matashi su kuma ayyana yanayi da fasalin da rayuwarsa za ta kasance da kuma irin kalubalen da zai fuskanta a makarantar gaba da sakandire.

Fashin Baki: Ta’arifin Matasa Da Makarantun Gaba Da Sakandire

Matasa jimlar kalmar matashi ce wadda ke nufin ‘yaro wanda ya fara balaga’, idan mace ce kuma sai a kira ta ‘matashiya’, (Kamusun Hausa: 339). Shekaru ne hanya mafi sauki ta fayyace ko wane ne matashi, musamman in an yi la’akari da shekarun neman ilimi da kuma samun aiki. Don haka, ‘matashi shi ne mutumin da yake tsakanin shekarun da zai kammala ilimin da ya zama tilas a kansa da kuma shekarun da ya sami aikinsa na farko. Duk da cewa wannan adadin shekaru yana tsawaita gwargwadon yawaitar rashin aikin yi da karancin dogaro da kai ga matasan.

Hukumar UNESCO ta bayyana ma’anar kalmar matashi dangane da muhallin da aka yi amfani da kalmar. Alal misali, idan batun da ya shafi kasa da kasa ne , ana amfani da ma’ana ta bai daya ta Majalisar Dinkin Duniya  inda aka bayyana matasa a matsayin mutanen da suke tsakanin shekaru 15 zuwa 24. www.unesco.org/new/en/social-and-human-sciences/…/youth/youth-definition/.

A batutuwan da suka shafi kowace kasa a karan kanta kuwa, alal misali idan za a gabatar da wani shiri na matasa a cikin al’umma, za a iya fahimtar ma’anar ‘matasa’ ta hanya mafi sauki. A nan, Hukumar UNESCO ta amshi duk ma’anar da kowace kasa ta ba kalmar. Za ta iya kasancewa kamar yadda Yarjejeniyar Matasan Afirka  ta bayyana matashi a matsayin ‘duk mutumin da ke tsakanin shekaru 15 zuwa 35.’

Su kuwa makarantun gaba da sakandire, makarantu ne da ake zuwa bayan an kammala karatun sakandire kuma an cika sharuddan shigarsu . Su ne mataki na karshe a tsarin makarantun boko. Irin wadannan makarantu sun hada da kwalejojin ilimi da kwalejojin kimiyya da kere-kere da kwalejojin share fagen shiga jami’a da kwalejojin horar da ma’aikatan kiwon lafiya da jami’o’i da sauransu. A irin wadannan makarantu ne ake samun horarwa da takardar shaidar difiloma da shaidar malanta da digirin farko da na biyu da kuma digirin digirgir. A irin wadannan makarantu ne ake yankar kadadar da za a sami kwarewa a yi ta nomawa a bokonce, domin samun abin masarufi na tafiyar da rayuwar yau da kullum. Shi ya sa Malam Aminu Alan Waka ya ce:

“Kun ga jami’a  ita at tushen al’umma,

Dukka shugaba daga can ne ke bullowa.

Kun ga likkita mai lura da masu cuta,Dagga jami’a ke zowwa babu musawa.

Ku mai da hankali kan hamshakin dansanda,Ya yi jami’a ba  mai suka da musawa.

Mu je ma’aikatar shari’a taron alkalai,Dagga jami’a kowannensu yake zowwa.

Ko a bangaren lauyoyi in mun lura,Jami’a suke tafiya sannan zakkowa.”

(Aminu Alan Waka: Wakar Jami’a, Rerawa ta 2)

Kalubalen Da Matasa Ke Fuskanta A Makarantun Gaba Da Sakandire Rayuwar matasa a makarantun gaba da sakandire cike take da kalubale ta fuskoki mabambanta. A wannan gabar, an yi wa duk kalubalen fyadar kadanya ne, aka zabi muhimmai daga cikinsu aka kasafta su zuwa gida hudu kamar haka;

Yanayin Da Dalibi Ya Taso a Ciki: Fandisho Da Tattalin Arziki

Yanayin da dalibi ya taso a ciki kamar yadda aka haska a sama, yana taimakawa wajen haifar da tasgaro a sha’anin rayuwarsa ta makarantun gaba da sakandire. Matsaloli irin su karancin fandisho mai kyau a firamare da karancin horarwa da kayan aiki a makarantun sakandire su ne suke taruwa su haifar da yanayin ya-na-iya-da-kaina ga matashin da ya shiga makarantar gaba da sakandire a karon farko. Da zarar ya shiga makarantar ma, nan wasu kalubalen da suka jibanci cinkoson dalibai a aji da karancin wayewar yadda zai fara su ma za su yi masa marhabin. Kafin ka ce me, lokaci ya kure masa. Tun farko daman bai taso a yanayin da zai sami jagorancin fahimtar irin rayuwar da ya tsinci kansa a makarantar ba, tun daga zabin irin kwas din da zai karanta da irin makarantar da zai shiga da kuma yadda rayuwa take a irin wadannan makarantu.

Ga ‘ya’yan masu karamin karfi, matsin tattalin arziki na haifar da rabe-rabe na neman wurin zama, ga kuma kalubalen tafiyar kasa ga wadanda suke zaune nesa da makaranta. Hakan yana shafar halartarsu aji a kan lokaci da kuma haifar da tasgaro ga fahimtar darussa da cin jarabawa. Ba ma wannan ba, hatta fafutukar biyan kudin makaranta da abin kalaci kalubale ne babba da (wasu) matasan ke cin karo da su a makarantun gaba da sakandire.

Ginuwar Kwakwalwa Da Bakon HarsheBature bai da niyyar raya  kowane harshe a duk kasar da ya kafa mulkinsa na yaudara in ba harshen Turanci ba. Alkiblar salon mulkinsa ita ce, rusa duk wani harshen da ke raye a al’ummar da ya ziyarta. Duk wani harshe da ya rayu bayan kafa ilimin boko ba da son ran Bature  ba ne.

Muradina a wannan fasali shi ne jawo hankalinmu cewa daga cikin ilimin boko Ingilishi shi ne kan gaba. Cikin kowane darasi Ingilishi tilas ne, wanda duk bai da shi bokonsa ba yardajje ba ne. Babban kalubalen matasanmu a makarantun gaba da sakandire shi ne yadda aka dauki Ingilishi a matsayin karatun fatiha ga liman a cikin sha’anin boko, ga shi kuma Ingilishin bai ishe mu ba. Da wanne dalibi zai ji? Aikin dai biyu ne a gabansa, fahimtar bakon harshen da kwakwalwarsa ba ta ginu a kansa ba tun kuruciya, da kuma fahimtar karatun da dole sai an fahimci bakon harshen . Wannan babban kalubale ne da ke mayar da matasanmu koma-baya cikin tsara a makarantun gaba da sakandire.

Zamu ci gaba mako mai zuwa….

Ana iya tuntubar mujahid ta:

mujaheedabdullahi@gmail.com

+2348069299109, +2348156747550

Exit mobile version