Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Ga Yadda Hukumar Zaben Ta Republican Ta Amurka Ta Tsara Shirin Yakar Kasar Sin

Published

on

Wani muhimmin matakin da gwamnatin Amurka ta dauka wajen boye kuskure da take yi da dora laifi ga kasar Sin. Bisa labarin da shafin Intanet na labaran siyasa na Amurka mai suna “Politico” ya bayar a kwanan baya cewa, ’yan jam’iyyar Republican na Amurka sun gabatar da wani bayani mai shafuka 57, don koyar da ’yan takararsu yadda za su dora laifi ga kasar Sin, lokacin da aka yi musu tambayoyi cewa, ko wannan laifin Donald Trump ne ko a’a? kuma ko wannan batu ya shafi manufar wariyar launin fata ne ko a’a.

Marubuci ya bada hanyoyi uku wajen yaki da kasar Sin. Na farko, shafawa kasar Sin bakin fenti wai kasar Sin ba ta bada labarai a bayyane, matakin da ya yi sanadiyyar barkewar COVID-19, da kuma zargin ’yan jam’iyyar Demokarat cewa, ba su dauki matakan da suka dace kan kasar Sin ba, har ma da ’yan jam’iyyar Republican za su gudanar da shirin yankewa kasar Sin hukunci saboda a ganinsu Sin tana da laifin yada cutar.

Abin lura shi ne, wadannan matakai ba ma kawai an yi amfani da su a lokacin yakar cutar ba ne. ’Yan jam’iyyar Republican sun nuna cewa, suna shirin maida kasar Sin a matsayin wani muhimmi batu da za a tattauna cikin zaben 2020. Alal misali, rukunin yakin neman ta zarce na Donald Trump ya gabatar da wani bidiyo kwanan baya, don bayyana cewa, dan takarar jam’iyyar Demokarat Joseph Robinette Biden yana sada zumunci sosai da kasar Sin.

An bada tabbaci cewa, matakan da ’yan siyasar Amurka suka dauka kwanan baya na da alaka sosai da abubuwan dake cikin wannan bayani, game da labaran da “Politico” ya bayar, mai magana da yawun kwamitin majalisar dattijai na jam’iyyar Republican Jesse Hunt bai musanta wadannan abubuwa ba.

Wasu Amurkawa suna mayar da wannan bayani a matsayin littafin karairayin Mitch Mcconnell, dan jam’iyyar Republican, kuma shugaban jam’iyyar dake da galibin kujeru a majalisar dattawan kasar Amurka. (Mai Fassarawa: Amina Xu)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: