Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Ga Yadda Kasashen Sin Da Afirka Suke Yakar COVID-19 Cikin Hadin Gwiwa

Published

on

Jiya Alhamis, cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afirka ta fitar da rahoton dake cewa, yawan mutanen da suka kamu da Korona, wato cutar numfashi ta COVID-19 a Afirka ya kai mutum 210,153, kana adadin mutanen da cutar ta hallaka a nahiyar ya kai 5,692, yayin da mutane 95,781 suka warke daga cutar.

Kuma bi da bi, kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin ta samar wa kasashen Afirkan sun isa kasashen nahiyar.
A ranar 11 ga wata, kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin ta samar wa kasar Sudan ta Kudu sun isa birnin Juba, fadar mulkin kasar. Wadannan kayayyakin yaki da cutar sun hada da kayan ba da kariya, da takunkumin rufe hanci da baki, da kuma maganin tantance cutar numfashi ta COVID-19 da sauransu. Wannan shi ne kayayyaki karo na hudu, da kasar Sin ta baiwa kasar Sudan ta Kudu tun daga watan Maris na bana.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sudan ta Kudu Mayen Dut Wol, ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin, dangane da taimakon da ta baiwa gwamnati da al’ummomin kasar Sudan ta Kudu.
A daren ranar 10 ga wata kuma, kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin ta samar wa kasar Mauritania sun isa kasar. A yayin bikin mika kayayyakin, wani jami’in kasar Mauritania ya bayyana cewa, taimakon da kasar Sin ta baiwa kasar sa, ya nuna kyakkyawan zumunci da hadin gwiwa mai dorewa dake tsakanin kasashen biyu.
Haka zakila kuma, a ranar 10 ga watan nan ne aka isar da kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 karo na biyu da gwamnatin kasar Sin ta samar wa jamhuriyar Nijer a birnin Yamai, fadar mulkin kasar. A wannan rana kuma, ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijer din, ya mika wadannan kayayyaki ga ma’aikatar kiwon lafiya da ma’aikatar harkokin jin kai da daidaita matsala bayan aukuwar bala’u ta kasar.
Ministan harkokin jin kai da daidaita matsala bayan aukuwar bala’u ta jamhuriyar Nijer Magagi Laouan ya bayyana cewa, kasar Sin ta baiwa Nijer taimako matuka a fannin kiwon lafiya da sauransu. Kuma kayayyakin yaki da cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin ta samar wa Nijer din na wannan karo, za su ba da tabbaci ga Nijer, wajen cimma nasarar yaki da annobar, lamarin da ya nuna kyakkyawan zumuncin dake tsakanin kasashen biyu.
Kana, wakilin hukumar kiwon lafiyar duniya (WHO) dake Nijer, ya yi godiya ga kasar Sin, dangane da taimakon da take baiwa jamhuriyar Nijer, da ma sauran kasashen duniya wajen yaki da annobar. Ya ce, kasar Sin ta zama abin koyi ga sauran kasashen duniya, kuma hukumar WHO za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Sin, da sauran abokanta na kasa da kasa, domin ba da taimako ga kasar Nijer, ta yadda za ta cimma nasarar yaki da cutar numfashi ta COVID-19.
Bugu da kari, a jiya Alhamis gwamnatin kasar Sin ta aike da kashi na biyu na tallafin kayayyakin kiwon lafiya don yaki da annobar COVID-19 ga kasar Zimbabwe yayin da a ’yan makonnin nan ake samun karuwar adadin masu kamuwa da cutar a kasar dake kudancin Afrika.
Kashi na biyu na kayan tallafin sun hada da takunkumin fuska da jami’an lafiya ke amfani da su kimanin 165,000, da rigunan ba da kariya wato PPE kimanin 25,000.
Jakadan kasar Sin a Zimbabwe Guo Shaochun, shi ne ya mika gudunmawar kayayyakin ga shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, a lokacin bikin mika kayan da aka gudanar a fadar gwamnatin kasar.
A jawabin da ya gabatar a lokacin bikin, jakadan na Sin ya ce, wannan gudunmawa ta kara nuna karfin abotar dake tsakanin bangarorin biyu. Bayan da gwamnatin Sin ta jagoranci bayar da tallafin, ragowar bangarori kamar bangaren sojojin kasar Sin, da kungiyoyin ’yan kasuwa da daidaikun jama’a dukkansu sun bi sahun gwamnatin, inda suke mika tallafinsu ga kananan hukumomi, da asibitoci, da makarantu, da marasa galihu.
Yayin da yake karbar tallafin, Mnangagwa ya bayyana godiyar da Zimbabwe ta nuna ga taimakon da Sin ke ci gaba da baiwa kasarsa. Ya ce tallafin yana da matukar muhimmanci wajen taimakawa kasar yaki da yaduwar annobar a kasar.
Mnangagwa ya ce, wannan taimako da yin hadin gwiwar za su taimaka matuka ga irin kokarin da kasar Zimbabwe ke yi a yaki da annobar kuma zai taimakawa jami’an lafiyar kasar cikakkiyar kariya yayin da suke gudanar da ayyukansu. (Masu Fassarawa: Ahmad Fagam, Maryam Yang)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: