CRI Hausa" />

Ga Yadda Likitocin Kasar Sin Suke Ci Gaba Da Yin Aiki A Congo Kinshasa A Yayin Da Ake Tinkarar Annobar COVID-19

A shekarar 1973 ce kasar Sin ta fara tura tawagogin likitocinta zuwa kasar Congo Kinshasa. Tawagar likitocin kasar Sin da yanzu suke aiki a kasar Congo Kinshasa, ita ce tawaga ta 19 da kasar Sin ta tura.

Ko da yake har yanzu annobar cutar COVID-19 tana yaduwa a duk fadin duniya, wadannan likitoci na kasar Sin sun yi ban kwana da iyalansu, sun tafi kasar Congo Kinshasa domin tallafawa kiwon lafiyar mazauna kasar, da Sinawa wadanda suke zaune a kasar.
Likitocin kasar Sin wadanda suke aiki a kasar Congo Kinshasa sun sha wahalhalu sosai sakamakon barkewar annobar CPVID-19. Shugaban tawagar likitocin kasar Sin dake Congo Kinshasa Mr. Wang Jiechao ya bayyana cewa, da bullar annobar a kasar Congo Kinshasa, asibitin sada zumunta tsakanin Sin da Congo Kinshasa, inda likitocin kasar Sin suke aiki, ya zama asibitin da hukumar gwamnatin kasar ta tabbatar yana karbar marasa lafiya wadanda suka harbu da cutar COVID-19. Ko da yake akwai hadarin harbuwar cutar, amma likitocin kasar Sin ba su dakatar da aikinsu ba, sun tsaya kan mukamansu na karbar marasa lafiya kamar yadda suka saba yi a da. A lokacin da suke kokarin kammala aiki na yau da kullum, sun kuma kaddamar da kwas na tinkarar annobar ga masu aikin jinya na bangaren Congo Kinshasa, har ma sun samar wa bangaren Congo Kinshasa kayayyakin kandagarkin annobar kyauta, domin yin namijin kokarinsu, wajen taimakawa bangaren Congo Kinshasa tinkarar annobar.
“Mun zanta da shugaban asibitinmu, mun bayyana masa shirinmu na bude wani kwas na ba da lacca, kan ilmin rigikafi, da kuma tinkarar annobar. A yayin kwas din, mun koyar musu fasahohin wanke hannu bisa matakai 7, mun kuma samar musu kayayyakin kandagarkin annobar, kamar takunkumin baki da hanci kyauta.”
Aikin da tawagar likitocin kasar Sin ta yi ya samu amincewa sosai a kasar Congo Kinshasa. Fasahohin jinya na gargajiya na kasar Sin, sun kuma samu amincewa daga wajen jama’ar wurin. Dr. Yan Zhihui, wani likitan tawagar, ya bayyana cewa, akwai likitoci masu aiki da fasahohin gargajiyar kasar Sin dake cikin tawagar likitocin kasar Sin da aka tura zuwa kasar Congo Kinshasa a karo na farko a shekarar 1973, a cikin asibitin sada zumunta tsakanin Sin da Congo Kinshasa, ana da sashen ba da allura bisa ilmin likitancin gargajiyar kasar Sin.
“Ana da sashen ba da allura bisa ilmin likitancin gargajiyar kasar Sin, a asibitin sada zumunta tsakanin Sin da Congo Kinshasa. A kowace tawagar likitocin kasar Sin da aka tura zuwa kasar Congo Kinshasa, ana da likitocin gargajiyar kasar Sin. Mazauna wurin suna amincewa da likitancin gargajiyar kasar Sin sosai. Sun san cewa akwai likitocin kasar Sin dake cikin asibitin, su kan kuma neme mu da mu yi musu allura, ko mu ba su maganin gargajiyar kasar Sin. Na zo nan tare da wani maganin gargajiya da wasu allurai, ina son kaddamar da wasu sabbin shirye-shirye a asibitin.”
A cikin shekaru kusan 50 da suka gabata, tawagogin kasar Sin da aka tura zuwa kasar Congo Kinshasa, sun je kasar tare da dimbin na’urorin aikin jinya da fasahohin jinya, sakamakon haka, fasahar jinya ta asibitin da suke ciki ta kuma kyautatu. Mr. Li Peng, wani likita wanda ke aikin kiwon lafiyar jarirai da yara, ya yi bayani cewa, ko da yake asibitin sada zumunta tsakanin Sin da Congo Kinshasa, na daya daga cikin asibitoci uku mafi kyau a kasar, amma na’urorin jinya da fasahohin ba da aikin jinya, suna kan matsayin su, kamar yadda wasu asibitocin kananan hukumomin kasar Sin suke.
A lokacin da likitocin kasar Sin suke yin mu’amala da ma’aikatan jinya na wurin, su kan koyar musu fasahohin ba da aikin jinya na zamani, domin kokarin kyautata kwarewarsu ta ba da jinya.
“Dukkan likitocin kasar Sin sun fito daga asibitoci mafi kwarewa a lardin Hebei na kasar Sin, sun kware sosai wajen ba da jinya, har ma suna da ilmomin zamani na aikin jinya. Bugu da kari, asibitocin da muke aiki da su a kasar Sin, suna da na’urorin zamani. Sabo da haka, mun yi kokarin samar musu wasu kyawawan kayayyaki, da fasahohi, da ilmomi na zamani na aikin jinya.” (Sanusi Chen)

Exit mobile version