Ga Yadda Wasu Namun Daji Suke Yawo Cikin ’Yanci A Kasar Sin

Daga Sanusi Chen

A kwanakin baya, wasu giwaye 15 wadanda suke yawo daga kudu zuwa arewa a cikin lardin Yun’nan dake kudu maso yammacin kasar Sin, sun samu karbuwa a duk fadi duniya.

Ga giwaye wadanda suka yi tafiya har ta tsawon kilomita 500 a lardin Yun’nan

Garin wadannan giwaye yana yankin Xishuangbanna dake kudancin lardin Yun’nan. An labarta cewa, a watan Maris na shekarar 2020, wasu giwaye 16, ciki har da wadannan sha biyar sun kafa wata tawaga sun soma kama hanyarsu zuwa arewa. A kan hanyar, wata giwa mace ta haifi wata karamar giwa, sannan a watan Afrilun bana, biyu daga cikin tawagar sun yi ban kwana da sauran giwaye sun koma garinsu.

Ga giwaye wadanda suka yi tafiya har ta tsawon kilomita 500 a lardin Yun’nan

Sabo da haka, yanzu tawagar tana kunshe da giwaye 15 wadanda har yanzu suke yawo a kai a kai a lardin Yun’nan.
Wadannan giwaye sun yi shekara 1 ko fiye suna yawo suna cin zango fiye da kilomita 500 daga yankin Xishuangbanna zuwa yankin Kunming, hedkwatar lardin Yun’nan.

A cikin wannan shekara daya ko fiye, suna yawo suna ci suna sha suna bude idanunsu.

Ga dabbar Tiger da ta shiga wani kauye a lardin Heilongjiang

Bisa dokar kare namun daji ta kasar Sin, duk wanda ya sadu da su, dole ne ya kare su, bai iya lalata su ba. Za a yanke hukunci kan duk wanda ya lalata su ko kashe daya daga cikinsu balle dukkansu. Bugu da kari, yanzu kowa ya sani, giwaye su kasance kamar abokan dan Adam ne, bai kamata a lalata su ko kashe su ba.

Sakamakon haka, ko da yake wadannan giwaye sun cinye kayan lambu da manoma suka noma, ko sun shiga gidajen dan Adam, sun ci kayayyakin abinci da aka adana a gida, babu wanda ya lalata su, sai dai sun gudu daga gidajensu domin magance saduwa da su a gida.

Ga tsuntsayen Red-crowned cane dake fadamar Yancheng na lardin Jiangsu

Sannan hukumomin kula da namun daji na lardin Yun’nan, har ma ta kasar Sin sun yi ta kulawa da su, sun koyarwa mutanen ilmin samar musu kayayyakin abinci, da dabarun magance saduwa da su.

Ga tsuntsayen Red-crowned cane da suke yawo a fadamar Cangzhou na lardin Hebei a watan Mayu.

Akwai wani labara mai ban sha’awa da ya faru kan wata karamar giwa daga cikinsu. Wata rana, wannan karamar giwa ta shiga wani gida ta ci abinci kusan kilo 200. Amma ba ta san wannan ba abinci na yau da kullum ba, shi ne abincin dake samar da “barasa”.

Sakamakon haka, ya bugu ya yi barci a gidan.

Ban da labari game da wadannan giwaye 15 wadanda har yanzu suke yawo cikin ’yanci a lardin Yun’nan, yanzu ga wani labari daban game da dabbar Tiger da ya faru a lardin Heilongjiang dake arewa masu gabashin kasar Sin.

A ran 23 ga watan Afrilun bana, ba zato wata dabbar namun daji ta Tiger ta kutsa cikin wani kauyen dake lardin Heilongjiang, sannan an cuce ta, an kai ta zuwa gidan kiwon namun daji domin binciken lafiyarta.

A wannan gidan renon namun daji na Heilongjiang, masu aikin kimiyya sun yi kwanaki 25 suna bincikar lafiyarta, da kuma sa ido kan yadda take rayuwa a daji. Bayan sun tabbatar cewa, tana cikin koshin lafiya, a ran 18 ga watan Mayun da ya gabata, an sako wannan Tiger, ta koma gandun daji. Amma har yanzu masu aikin kimiyya na kasar Sin suna amfani da na’urorin zamani suna kulawa da ita, domin sanin yadda take rayuwa a gandun daji kamar yadda ake fata.

An labarta cewa, yayin da wannan tiger ta shiga kauyen, ta sadu da wata mace Li Chunxiang, wadda take aiki a gona. Da bullowar wannan tiger, sauran manoma wadanda suka ga wannan damisa, sun kira Li Chunxiang da kakkausar murya, amma ba ta ji ba. Bisa taimakon wani manomi daban, an cuci Li Chunxiang wadda ta ji dan jikkata a sassa biyar na jikinta. Yanzu wannan mace ta samu sauki ta fito daga asibiti ta koma gida.
Bugu da kari, ga wani Karin labara daban game da wata tsuntsu da ake kiran shi “Red-crowned crane” cikin harshen Ingilishi.

Wannan labari ya kuma faru ne a lardin Heilongjiang. A ran 29 ga watan Mayun da ya gabata, wata tsuntsu “Red-crowned crane” ta sauka a cikin wani kauye ta tsaya a kan hanya ta hana tafiye-tafiyen mutane. Babu sauran zaba, sai dai mutane sun magance saduwa da ita, sun leka ta daga nesa kawai, sabo da bisa dokar kare namun daji ta kasar Sin, ba a iya lalata irin wannan tsuntsu na “Red-crowned crane” ba.

An labarta cewa, a hakika dai, tsuntsayen “Red-crowned crane” dake lardin Heilongjiang su kan yawo a yankunan kauyuka. Wani lokaci, sun ci kifayen da ake sayarwa a gefen titi.

Masu aikin kare namun daji na kasar Sin sun bayyana cewa, dalilin da ya sa tsuntsun “Red-crowned crane” ya shiga birni ko kauye shi ne, mai yiyuwa ne tana neman “soyayya”.

An labarta cewa, tsuntsun “Red-crowned crane”, dabba ce dake kusan karewa a duk fadin duniya. Kawo yanzu, jimillar tsuntsyen “Red-crowned crane” ta kai wajen dubu 2 kawai a duk fadin duniya. Sabo da haka, kasar Sin ta fitar da dokar kare su, har ma ta kebe wata fadamar dake yankin Yancheng na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin, inda tsuntsayen “Red-crowned crane” wajen dubu 1 suke da zama. Wannan fadama ta riga ta zama fadama mafi girma a duk duniya inda tsuntsayen “Red-crowned crane” suke da zama a lokacin sanyi. A tsakanin watan Nuwamban kowace shekara zuwa watan Maris na shekara mai zuwa, a kan ga dimbin tsuntsayen “Red-crowned crane” suke shawagi a sararin saman yankin Yancheng.

Bugu da kari, a kwanan baya, a cikin wata fadama daban dake bakin tekun Huanghai a yankin Cangzhou na lardin Hebei dake arewacin kasar Sin, ba zato ba tsammani an gano tsuntsayen “Red-crowned crane” guda biyar wadanda suke yawo a cikin fadamar. Yau shekaru 10 da suka gabata ne, an taba ganin tsuntsun “Red-crowned crane” a cikin wannan fadama.

Exit mobile version