Daga Khalid Idris Doya
Kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ya shaida cewar manoman da Boko Haram suka kashe a ranar Asabar sun je gona ne ba tare da samun izinin amincewar zuwansu daga wajen sojoji ba.
Ya na mai cewa rashin samun izinin ne ya sanya ‘yan ta’addan suka yi amfani da wannan damar wajen kai musu hari tare da kashesu, yana mai cewa akwai yankunan da har zuwa yanzu suna fuskantar hatsarin shiga lura da cewa ‘yan Boko Haram ka iya barazana a kowani lokaci ga yankunan.
Ya ce, yankuna da dama da Boko Haram ke aikata ta’asarsu, ana takatsantsan din shiga wanda jama’a da dama sun san hakan.
Da aka tambashi shin ko ya na sukar manoman da suka rigamu gidan gaskiya ne sai ya amsa da cewa, “A’a ba haka nake nufi ba, amma maganar gaskiya Shin sojoji da ke kula da yankin sun amince? Ko wani daga cikinsu ya nemi izini kafin ya ci gaba da aiki? Shugabannin sojoji sun fada mani cewa ba su nemi shawara ba, saboda haka wannan damar ‘yan ta’addan suka yi amfani da ita wajen kai musu hari,”
“Ya kamata a ce sojoji sun amince tukunna kafin a ci gaba da ayyuka a yankunan.”
Ya ce, “Gwamnati ta ji zafin wannan ta’addancin da ya farun. Kisan manoma 43 abun kaito ne sosai. Ya kamata jama’a su sani akwai yankunan da shigarsu na da hadari sosai.
“Mafiya yawan wadannan yankunan an cetosu ne daga ‘yan ta’addan Boko Haram, akwai wurare da dama da har yanzu ba a samu amincewan jama’an kauyukan su koma ba. Wadannan wuraren suna bukatar idan mutum zai shiga noma ko kiwo ya nemi amincewar sojoji kafin komawa ko zuwa.”
“Idan jama’a sun shirya komawa wurarensu, ya kamata su nemi amincewa kafin komawa,” Inji Kakakin shugaban.
LEADERSHIP A YAU ta labarto cewa kisan manoma 43 ya janyo korafe-korafe da kirayen a dauki mataki, inda wasu manoma shida suka jikkata a ranar Asabar yayin da suke noma a cikin gonan shinkafa a kauyen Koshebe da ke jihar Borno.
Wasu masu sukar nasa har da fadan munanan kalamai a kansa dukka a kafafen sadarwar zamani, sai dai Garba Shehu a cikin hirar ya nuna cewa shi ba wai kushe manoman yake ba illa dai fadin gaskiyar cewa ba su nemi izinin shiga gonan ba.