Connect with us

LABARAI

Gadanya Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar Lauyoyi Na Kano

Published

on

Kungiyar Lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano ta gudanar da zaben shugabanninta a sakatariyar kungiyarta da ke kan titin Guda Abdullahi a ranar Litinin 29 ga Yuni, 2020.

Zaben na shugabanin kungiyar na matakai guda 12 ne, sai dai an sami wasu ’yan takara da ba su da abokan yin takara.

Guraben da a ka yi takara a kansu sun hada da kujerar neman shugabancin jam’iyyar da mutane uku su ka yi takara da neman kujerar mataimakin sakatare, wanda mutum biyu su ka yi ma ta takara da neman takarar jami’in hulda da jama’a shi ma mutum biyu su ka nema.

Bayan kammala zaben, Shugaban Kwamitin zaben, Barista Tajuddeen, ya ce, ‘yan takara da dama sun shiga zabe, amma mafi mahimmanci shi ne Malam Aminu Sani Gadanya ya lashe zaben da kuri’u 214 a kan abokan takararsa.

Ya ce, zabe an yi cikin lumana bisa samun hadin kan ’yan takara. An yi takara a kan mukamai 12, sai dai guda biyar ne a ka kai ga kada kuri’unsu; sauran sun yi nasara ba hamayya. Amma wasu daga cikin wakilan ’yan takara sun yi korafi da cewa an sami karin kuri’u.
Advertisement

labarai