Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTAUNAWA

Gadon Siyasa Da Kasuwanci Na Yi – Hon. Mai-Shanu

by Sulaiman Ibrahim
January 14, 2021
in TATTAUNAWA
5 min read
Gadon Siyasa Da Kasuwanci Na Yi – Hon. Mai-Shanu
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

HON. MUHAMMAD UBA GURJIYA MAI SHANU shine wakilin al’ummar karamar Hukumar Bunkure a Majalisar Dokokin Jihar Kano, tsohon malamin makaranta, matashin dan siyasa kuma ‘yan gaba dai gaba dai masu rajin kare kimar Gwamna Ganduje na Jihar Kano da Jam’iyyar APC. A tattaunawarsa Da Wakilin LEADERSHIP A YAU, ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, Hon. Mai-Shanu ya jinjina wa kokarin Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Dr. Ganduje, sannan ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da yake tunkaho da su a tsawon shekarun da ya yi yana hidimta wa al’ummar da yake wakilta. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:

Za mu so ka gabatarwa da mai karatu kanka da kanka?
Alhamdulillah kamar yadda aka sani ni Sunana Honarabul Muhammad Uba Gurjiya Mai Shanu, an haifi ni a garin Gurjiya dake karamar Hukumar Bunkure a Jihar Kano cikin Shekara ta 1982
Na halarci makarantar firamare, daganan naje garin Bunkure inda na samu damar fara karatun karamar Sakandire, bayan nan na wuce Makarantar koyon harshen larabci SAS dake birnin Kano Inda na kammala karatun babbar sakandire, Domin ganin an dan kara fadada Karatu na shiga makarantar ilimin koyarwa mai zurfi ta Sa’adatu Rimi College of Education dake Kano inda na samu shaidar karatu na NCE

Daga nan kuma fa sai ina aka fuskanta?
Alhamdulillahi daganan sai na fara aikin koyarwa a makarantar firamaren Tugugu a Bunkure domin fara bayar da irin tamu gudunmawarWanda hakan ya bani damar koyarwa  a firemare tsawon shekara uku. Saboda haka bayan  taba koyarwa na Shekara uku ne cikin ikon Allah na samu sukunin shiga jami’ar Bayero dake Kano Inda na samu digirin farko a fannin ilimin manya da rayuwar al’umma.  Bayan kammala digiri na na farko sai na koma na cigaba da koyarwa har tsawon shekara goma sha hudu. Haka Kuma nayi Amirul Hajji na karamar Hukumar Bunkure tsawon shekara hudu. Alhamdulillah wannan shi ne dan takaitaccen tarihin karatu. Amma kamar yadda aka sani yana daga tsarin tarbiyyar musulunci duk wani da da ya samu kyakkyawar tarbiyya, wajibi ka sa meshi ya yi karatun Allo da ilimin littattafan addini gwargwadon abinda Allah yasa ya rabauta da shi.

samndaads

Hon. kasancewar ka fito daga gidan Kasuwanci da siyasa, ko ya gwagwamaryar rayuwarta kasance?
Gaskiya ne kamar yadda aka sani Mahaifina gogaggen dan Kasuwa ne, sannan kuma dan siyasa ne fitacce, don haka na fara harkar kasuwanci tun ina karami inda na fara cinikin wake daga Kasuwar Anchau ina kawowa cikin birni na sayarwa, nayi kumar harkar ciniki takalma, nayi dillacin man fetur, ma’ana sayo shi daga Fatakwal zuwa Kano a karkashin Kamfanin mu na Gurjiya Enterprises, daganan kuma dai har zuwa yanzu ana ci gaba da harkar Kasuwanci. Domin mu a gidanmu ba zai yiwu yaro ya tashi ba sana’ar yi ba. Wannan itace kyakkyawar tarbiyyar da har zuwa yanzu ke zamar mana fitilar dake haske mana duk inda zamu tsoma kafarmu a rayuwa.

Tunda mun ji irin yadda aka samarwa rayuwa kyakkyawan tubali, shin ranka ya dade ya batun siyasa kuma?
Alhamdulillah na fara siyasa tun ina karamin yaro alokacin SDP, Ina tabbatar maka da cewa mu siyasa,  Addini da Kasuwanci gadonsu  muka yi, siyasa bude ido nayi a dakin mahaifiya na ga fasta. Tun muna kananan yara mu ake turawa cikin gidaje muna kai sakonni tare da wayar da kan iyaye mata da sauran al’ummar gari kan wanda ake son zaba da kuma Jam’iyyar da za’a zaba. Daganan muka fara bada irin tamu gudunmawar a jam’iyyu daban daban da muka tsinci kanmu a ciki. Wadda saboda kwazo da hazaka na jagoranci kungiyoyi daban daban a siyasan ce a karamar Hukumar Bunkure tun daga Shekara ta 2003 har zuwa 2007. Daga nan ne kuma Allah ya kaddara min yin takarar kujerar Wakilin Al’ummar karamar Hukumar Bunkure a Shekara ta 2015 na kuma samu nasarar lashe zaben, sannan a shekara ta 2019 na kara tsayawa wannnan takara kuma Allah ya sake bani nasara, mukamin Dana ke kai zuwa yau da muke wannan tattaunawar daku.

Wadanne irin nasarorin aka cimma zuwa yanzu?
Da farko muna kara yiwa Allah godiya, musamman irin hadin kan da Gwamna Ganduje ke baiwa wannan majalisa, wanda hakan ke bamu damar cin nasara aduk ababuwan da aka sa gaba. Sannan kuma muna samu cikakken hadin kan bangaren zartarwa wanda daman gimshikai uku ne ki rike da Gwamnatin siyasa, wadanda suka hada da bangarenmu na majalisar dokoki, bangaren zartarwa da sashin shari’a, kuma alhamdulillahi kowane bangaren na bayar da dukkan hadin kan da ake bukata domin ciyar da Jihar Kano gaba. Wannan ya hada da nasarar da na samu a kwamitin kudi wanda nayi kokarin samar da tsarin bibiyar yadda ake tattara haraji da kuma sarrafa abinda aka samu, samar da hanyoyin kara inganta harkar kudaden shiga, inganta  kananan kamfanoni da masana’antu, samar da kudurin da ya samu goyon bayan a bokan aiki inda aka dauki kwararrun Malamai mata a Jihar Kano, sannan mun samar da tsarin inganta fasalin magudanun ruwa da inganta muhalli da Inganta tsarin bin ka’idojin kashe kudaden Gwamnati. Haka lamarin samar da hasken wutar lantarki a titunan Kano, akwai batun rigimar Fanisau, Kasuwar Dawanau Wanda tuni Gwamna ya amince aka warware wannan rigingimu, haka batun titin Yahaya Gusau da sauran Ababuwan da Lokaci ba zai bari ba. Sai kuma ababuwan da a halin yanzu ake kansu, musamman tabbatar da ingancin tassawirar birnin Kano domin Inganta dokokin da aka samar domin bunkasar Kano, za’a samar da karin kasuwanni tare da samawa kananan ‘yan kasuwa musamman, ‘Yan tebura wanda suma ‘yan kasa ne kamar kowa. Saboda Haka wannan ke kara sa wannan Gwamnati himmatuwa wajen fadada kasuwanni, inganta magudanun ruwa tare da gyara hanyoyin kasuwannin mu da kuma uwa Uba bin doka da Oda.

Hon. kasancewar ka Wakilin al’ummar Bunkure, shinko me zaka ce kan tagomashin da al’ummar Bunkure suka amfana daga wakilcin da kake masu?
Alhamdulillah Allah shi ne shaida ban so ace ni aka yiwa wannan tambaya ba, domin kar na zama magori wasa kanka da kanka, Amma duk da haka jama’ar Bunkure shaida ne daga lokacin da dana zama wakilinsu a Majalisar dokokin Jihar Kano, akwai ababuwa masu yawa da muka kawowa wannan yanki namu, daga ciki akwai aikin hanyar karfi zuwa Bunkure, Rano har zuwa Kibiya. Baya ga wannan kuma na samu nasarar raba tallafin injunan ban ruwa sama da 500, takin zamani sama da buhu dubu goma sha biyu, daukar nauyin karatun yara mata likitoci da biyan kudaden jarrabawa, raba jari da koyar da sana’u iri daban daban ga mata da matasa, raba jari ga maasa 500 da aka rabawa Naira dubu goma goma, samar da tallafi ga jami’an tsaron da suka hada  da ‘yan Sanda, cibil defence, bigilanti da kuma hada kai da iyayen kasa kama daga Hakimi, dagatai, masu unguwanni da limamai. Sai kuma tallawa al’ummar Bunkure domin rage radadin rufe gari da akayi sakamakon annobar Korona wanda na samar da tallafin buhun shinkafa buhu 600, katon na taliya 12,000, sai kuma  hasafin kudaden da muka tallafawa ‘yan asalin karamar Hukumar Bunkure dake zaune a wasu jihohin dab a Jihar Kano, na raba Babura sama da 50, shanu domin inganta harkar Noma guda 200 duk domin min mukara farantawa al’ummar da suka sahale mana wannan wakilci.

A karshe mene sakon ka ga al’ummar karamar Hukumar Bunkure?
Madallah, sakona da farko godiya zanyi bisa aminta da suka nuna min wajen damka amanar wakilcinsu, kuma da yardar Allah ba zan basu kunya ba. Sannan ina kara kira da babbar murya wajen kara bada dukkan goyon bayan da ake bukata ga wannan Gwamnati karkashin Jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, musamman ayi fitar dango domin zabar ‘yan takarkarunmu a zaben kananan Hukumomin dake gabatowa tare da ci gaba da addu’o’in dorewar zaman lafiya a karamar Hukumar Bunkure, Jihar Kano da kasa baki daya.

Mun gode.
Ni ma na gode kwarai da gaske.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kamfani Zai Cigaba Da Tallafa Wa Kananan Manoman Masara A Nijeriya

Next Post

Canjin APC Ko Canjin Rigar Mahaukata?

RelatedPosts

Amanar

Muna Son Buhari Ya Dauki Mataki Kan Maciya Amanar APC – Hon. Kibiya

by Muhammad
2 days ago
0

HON. YUSUF ADO KIBIYA tsohon dan siyasa ne, wanda ya...

Gwamna Inuwa Ya Bai Wa Matan Gombe Damar Tsunduma Siyasa – Hauwa Sarki

by Muhammad
2 days ago
0

HON. HAUWA ADAMU SARKI kansila ce mai wakiltar gundumar Dawaki...

Almajiran

Kama Almajiran Sheikh Dahiru Bauchi Bai Dace Ba – Sa’id Bin Usman 

by Muhammad
3 days ago
0

Tun bayan kama almajiran Sheikh Dahiru Usman Bauchi da gwamnatin...

Next Post
APC

Canjin APC Ko Canjin Rigar Mahaukata?

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version