Connect with us

RAHOTANNI

Gagarimin Taron Masoya Sayyada Fatiha Ya Gudana Cikin Lumana

Published

on

Alhamdulillah, bayan godiya da yabo da salati da sallamawa,  makasudin wannan taron dai shi ne, domin a kara caza zukatan masoya ta ganin an kwana biyu ba a ga fuskokin juna ba.

Shin mutanen Kano ne kawai ko har da na Abuja ne? A’a, an sami halartar jihohi da dama a fadi Nijeriya.

Mene ne abin da aka karantar a gurin? Da farko dai, sha’irai sun barje guminsu kamar irin su Sayyadi Rabi’u taka lafiya da Sayyadi Kabiru maulana da Sayyadi M. Jamilu K/waika da Bashir dan Musa da Sayyadi Ahmad Sirrin fatahi da Sayyadi Ahmad Abdallah da  Sayyadi Buzun ma’aiki da Sayyadi Abubakar sha’ir da Sayyda Zabiyar  Fayra da Sayyada Zainab Ambato da Sayyada Fatin Fada, kai a gaskiya ba zan iya lissafo su duka ba. Akwai kuma manyan shehunnai kamar irin su Sheik Ibrahim Mansur Kaduna da Sheik Abdurrazak Abuja da dai sauransu manyan shehunnai.

An dai gudanar da majalasi a kan hadin kan ‘yan’uwa tun daga kan fayra da zaburar da matasa wajen neman ilimin addini da na zamani da rikon da ibada da koyi da ayyukan bayin Allah da zaburar da matasa wajen yin sana’a domin dogaro da kai.

Daga karshe an bayyana mana kadan daga cikin halayen Sayyada Fatiha Inyas (RTA) irin kokarinta wajen yada addini da fayra da jarimta da hakuri da taimakon al’um da hada kan ‘yan’uwa da irin ayyuka mahaifinta Shehu Abubakar Bini Hashim da mahaifiyarta Sayyada Ummul Khairi da irin ayyukan kakanta Shehu Ibrahim Inyas (RTA).

Wannan taron ya gudana ne a karkashin jagorancin kahon zuciyar Sayyada Fatiha Inyas, Sheik Aliyu Sise Khalifa da Shugaban Halara Alhaji Salisu Yaro da fayra da Sayyadi Shukaranu Hadimin Halara da Sayyadi Dan Wali da Sayyadi Fatihu Yariman Sayyada da Sayyadi Rabilu da dai sauran su. Su ‘yan’uwa na soyayya da koyi da dabi’un abin da kake so Allah ya ci gaba da maimai ta mana irin wannan taron na masoya Sayyada mu kara samun farin ciki da anna shuwa bayan kammalawa. An tafi ziyarar ‘yan’uwa kamar yadda Sayyada ta saba gudanarwa idan ta zo.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: