Gaidam Ya Kafa Tarihi A Fagen Bunkasa Ilmi A Jihar Yobe — Hon Lamin

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Kwamishina Ilmin Jihar Yobe, Alhaji Mohammed Lamin ya bayyana cewa Gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Gaidam ya kafa tarihi wajen bunkasa sha’anin ilimin jihar ta hanyar ginawa da gyara manya da kananan makarantun jihar tare da kayan aikin koyarwa. Bugu da kari kuma, ya kara da cewa gwamnatin dauki ingantattun matakai wajen kyautata yanayin jin dadin malamai a kowanne mataki wajen biyan albashi a kan kari kana da biyan hakkokin wadanda lokacin ritayar su ya yi.

Hon Muhammad Lamin ya fara da bayyana cewa, “jihar Yobe tana daya daga cikin jihohin yankin Arewa Maso-Gabas wadanda rikicin Boko Haram ya yiwa mummunan lahani, inda baya ga salwantar dubun-dubatar rayuwar al’ummar jihar ciki har da daliban jihar. Wannan ya jawo koma baya a bangaren ilimi bisa ga yadda maharan suka ringa kai munanan hare-hare a makarantu tare da jawo hasarar rayukan daliban jihar. Kuma wannan jafa’i ta shafi kusan kowanne yankin jihar. Gwamnatin jihar ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen kokarin sauke nauyin da ya hau kan ta tare da zare dantse inda sake gina makarantun firamare sama da 24 da gina ajujuwa sama da 400. A bare guda kuma da samarda isassun kayan koyarwa tare da katange mafi yawan su domin inganta tsaron makarantun.”

“Har ila yau, makarantun da suke a yankunan kananan hukumomin Gujba, Gulani, Damaturu, Tarmuwa, Yunusari da Geidam, su ne suka fi dandana kudar wannan bahallatsar kona wa da rusawa baki daya duk da makarantu dake yankin Gujba da Gulani kuma sun fi sauran, saboda nasu ruguzawa ne baki daya zuwa toka. Amma duk da hakan, gwamnatin jihar Yobe ta sake gina su zuwa sabbi, fil”. In ji kwamishinan.

Bugu da kari kuma ya ce, a wancan lokacin, alkaluman da muke da su sun nuna cewar a Gujba da Gulani, baki daya yan ta’addan sun ragar-gaza su zuwa kufai. Dangane da hakan, sake gina wadannan makarantun da Boko Haram suka rusa ya fi karfin gwamnatin jihar Yobe ita kadai, bisa ga haka kuma ta nemi tallafin gwamnatin tarayya da kungiyoyin bada agaji tare da dai daikun masu bada jinkai domin sake farfado da ilimin jihar. Duk da wannan, gwamnatin Yobe bata karaya ba, a haka ta tunkari matsalar kuma ta ci galabar ta cikin nasara.

Exit mobile version