Gaidam Ya Yaba Wa Kungiyoyin Bayar Da Tallafi Ga ‘Yan Gudun Hijira

Daga Muhammad Maitela,

Gwamnan jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya yaba da tallafin jinkai da kungiyoyi ke bayarwa ga ‘yan gudun hijira a jihar, tare da bayyana cewa akwai bukatar yin aiki tukuru wajen yuwuwar mayar da ‘yan gudun hijirar zuwa yankuanan su na asali, domin su ci gaba gudanar da rayuwa kamar yadda suka saba.

Gaidam ya yi bayyana haka ne a sa’ilin da babban Darakta hukumar bunkasa abinci ta duniya (WFP) a Nijeriya; Misis Myrta Kaulard, ta kai masa ziyara a babban birnin jihar dake Damaturu.

Ya bayyana cewa dangane da yunkurin da gwamnatin jihar Yobe ta yi a bangaren, hadi da sauran kungiyoyin bayar da agajin gaggawa. Ya ce akwai bukatar a sake zare dantse da kara tallafi wajen saukake wa ‘yan gudun hijirar yanayin rayuwa.

“Wannan kira dangane da sake duba yuwuwar mayar da jama’ar zuwa muhallin su ya zo ne bisa la’akari da irin karin ayyukan jinkai da aka gudanar wa wadanda kuma zasu karfafa gwiwa ga ‘yan gudun hijirar jihar Yobe hadi da wadanda tuni sun koma da zama a cikin garuruwan su na asali.” Inji shi.

Haka kuma, Gaidam ya yaba da kokarin hukumar WFP da ta raba tallafin Mayan abinci ga kananan yara 17,000 domin rage matsalolin karancin abinci mai gina jiki ga yara a jihar. Ya sake nuna farin cikin yadda hukumar ta tallafa da kayan abinci da na noma ga magidanta kimanin 7,000 a kananan hukumomin Gujba da Gulani wadanda suka fi fuskantar matsalar tsaro a jihar.

Bugu da kari kuma, Alhaji Ibrahim Gaidam ya yaba da kokarin yan kwamitin da aka damka wa alhakin kula da sake farfado da yankunan ‘yan gudun hijirar, a karkashin mataimakin gwamnan jihar Alhaji Injiniya Abubakar D Aliyu.

Ya ce gwamnatin jihar Yobe bata taba samun wani koke ko rahoton karkata kayan masarufi da na abinci wanda aka ware domin ‘yan gudun hijira wadanda rikicin Boko Haram ya shafa. Ya ce wannan babban abin alfahari da bugun kirji ne.

Misis Kaulard ta ce makasudin zuwan ta a jihar shi ne domin ta samu kafar tattaunawar hadin gwiwa da gwamnatin jihar Yobe domin gudanar da aikin bai daya wajen lalabo tudun dafawa wajen sake farfado da yankunan ‘yan gudun hijirar jihar.

“hukumar bunkasa abinci ta duniya ta ziyarci jihar Yobe domin yin musayar yawu da shawarwari tsakanin ta da gwamnatin jihar Yobe, a bangarorin da suka shafi hada hannu wuri guda wajen farfado da lamurran ‘yan gudun hijira a wannan yanki “. In ji ta.

 

Exit mobile version