Gajartar Amarya Tasa Ango Ya Fasa Auren Amaryarsa Ana Tsaka Da Gudanar Da Biki
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gajartar Amarya Tasa Ango Ya Fasa Auren Amaryarsa Ana Tsaka Da Gudanar Da Biki

byMuhammad
3 years ago
Gajarta

Wata budurwa ’yar kasar Tunisiya da take shirin zama amarya ta rika samun sakonnin tallafi daga sassan duniya bayan an yi watsi da bikin aurenta lokaci guda saboda sukar da surukarta ta yi mata cewa ba ta gamsu da yadda kamanninta yake ba.

Aminiya ta rawaito cewa, a karshen watan jiya ne wata budurwa mai suna Lamia al-Labawi, ta wallafa labari mai ban-tausayi a shafin Facebook inda ta bayyana yadda abin da ya kamata ya zama mafi alheri a rayuwarta ya koma wani mafarki mai ban tsoro.

  • Kasar Sin Ta Mika Wasu Takardun Amincewa Da Yarjejeniyoyi Biyu Ga ILO
  • Yadda ‘Yan Bindiga Suka Hallaka Ma’aikata Hudu Da ‘Yansanda Biyu A Kamfanin Sarrafa Tasa

Ya kamata a ce an yi aurenta da angonta shekara hudu da suka wuce amma sai yanzu; an shirya komai kuma sun kashe makudan kudi don ganin komai ya tafi yadda aka tsara, amma abin da ba su yi la’akari da shi ba, shi ne furucin mahaifiyar ango.

Lamia ta ce, ba ta taba haduwa da mahaifiyar angonta ba, kuma maimakon a yi mata tarba cikin mutunci zuwa cikin danginsu, abin da ta samu a ranar aurenta shi ne munanan kalamai.

Bayan fara bikin daurin auren, baki sun hallara, surukar Lamia da wasu sun kudiri wani abu a zuciyarsu.

A gaban kowa, surukar ta matso kusa da danta (angon) ta ba shi umarnin ya soke bikin auren, tana mai cewa amaryar “gajera ce kuma mummuna” da ba ta cancanci ta auri danta ba.

A baya hotunan Lamia ne kawai ta gani, kuma da alama ta ji takaici sosai bayan ganin amaryar ido da ido.

Cin mutuncin da uwar angon ta yi wa amaryar bai zama wani babban al’amari ba, sai dai bakin sun yi mamakin abin da angon ya yi.

Ya bi umarnin mahaifiyarsa, kuma duk rokon da mutane da yawa suka yi a wurin bikin, amma ya watsar da auran Lamia ya bar harabar bikin tare da mahaifiyarsa.

Nan da nan labarin ya bazu a shafukan sada zumunta, kuma Lamia al-Labawi ta fara samun sakonnin goyon baya daga mutanen da suke gaya mata cewa, ta dage ta kuma gane cewa angon bai cancanci yin aure ba.

“Tare da soyayya da ’yan uwantaka, ina gaya muku, ku daga kanku ku fuskanci duniya da dukkan karfinku,” Dan wasan kwaikwayo na Tunisiya, Hedi Al-Mejri, ya rubuta wa Lamia.

“Duniya tana dauke da darasi, kuma dole ne mutum ya bambance tsakanin miji da sauran maza. Ubangijina zai saka mata da alheri, insha Allahu za ta samu abu mai kyau a gaba.

“Auren Lamia darasi ne daga darussan rayuwa, kuma gaba ta fi kyau, insha Allahu,” wani mai suna Sana Cherif ya rubuta a Facebook.

Lamia al-Labawi ta fitar da wani faifan bidiyo tana gode wa kowa kan kalaman karfafa gwiwa da suka aike mata. Abin da za a iya cewa game da angon shi ne, akalla bai yi watsi da auren a kashin kansa ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano
Al'ajabi

Matashi Ya Kashe Kakanninsa Kan Abinci A Kano

September 25, 2025
Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye
Al'ajabi

Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye

September 17, 2025
Dan Sanda Ya Kashe Abokin Aikinsa Da Almakashi Har Lahira A Kebbi
Al'ajabi

Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo

September 16, 2025
Next Post
An Bude Bikin Fina-finai Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 Na Birnin Beijing

An Bude Bikin Fina-finai Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 Na Birnin Beijing

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version