Galatasaray Tana Magana Da Arsenal A Kan Elneny

Kungiyar kwallon kafa ta Galatasaray dake kasar Turkiyya ta fara Magana da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal domin sayan dan wasan tsakiyar kungiyar, Muhammad Elneny, dan asalin kasar Masar domin ya koma kasar Turkiyya da buga wasa.

Zakarun na kasar Turkiyya sun sayar da dan wasansu na tsakiya, Fernando, zuwa kungiyar kwallon kafabta Sebilla kuma suna ganin Elneny, shi ne wanda zai iya maye gurbin dan wasan da suka sayar.

Kamar yadda rahotanni daga kasar Ingila suka tabbatar ana nan ana tattaunawa tsakanin wakilin kungiyar ta Galatasaray, Sukru Hanedar da wakilan kungiyar Arsenal a birnin Landan domin ganin cinikin ya tabbata.

Elneny dai bai bugawa Arsenal wasanta na farko ba da kungiyar kwallon kafa ta Newcastle a satin daya gabata kuma a kakar wasan data gabata wasanni biyar kacal aka fara da shahararren dan wasan wanda ya koma Arsenal daga Basel ta kasar Switzerland

A kwanakin baya ne dai a kasar Masar ‘yan sanda suka gano wata gawa wadda aka bayyana cewa an tsince ta ne a wani gidansa da yake ginawa wanda kuma ba a kammala ba sai dai ‘yan sanda a kasar sun bayyana cewa suna cigaba da bincike.

Elneny ya wakilci kasar Masar a gasar cin kofin nahiyar Africa da aka buga a kasar duk da cewa bai buga wasanni da yawa ba amma yana daya daga cikin kwararrun ‘yan wasan kasar da suka taka rawar gani a gasar.

Exit mobile version