Mahdi M Muhammad" />

Gamayyar Zaman Lafiya Ta Dattawan Arewa Ta Mayar Da Martani A Kan Tsadar Kayan Masarufi

Tsadar Kayan Masarufi

Dattawan Arewa sun alakanta tsadar kayan masarufi da ake fama a ita a kasar nan ga tabarbarewar harkokin tsaro, wadda ta sa zai yi matukar wahala manoma su iya safarar kayan gona daga wani yanki zuwa wani.

Dattawan sun bayyana cewa, matsalar tsaro a arewa tana haddasa yawan asarar rayuka, satar mutane, fashi da makami da sauran munanan laifuka a kullum, wanda kuma ba ma gabadaya ake sani ba.

A ranar Litinin ne dai Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta bayar da rahoton cewa, hauhawar farashin kayan abinci ya tashi zuwa kashi 17.38 a watan Oktoba, daga kashi 16.66 na watan Satumba.

A cikin wata sanarwa da shugaban gudanarwa na Gamayyar Dattawan Arewa Domin Zaman Lafiya (CNEPD), Zana Goni, ya fitar a jiya, ya yi kira da a sake fasalin tsarin tsaron kasar nan, don inganta harkokin al’umma na yau da kullum. Dattawan sun yi takaicin cewa manyan hafsoshin sojoji sun maida hankali wajen dakile masu zanga-zangar #EndSARS, fiye da batun tsaron rayuka da dukiyoyin arewa musamman bangaren maso gabas.

Sanarwar ta ce, “Muna son bayyanawa a nan cewa, lamarin na ranar lahadi, wanda ya dauki hankali a manyan wurare, kadan ne daga abin da muke gani a kullum a wasu sassan yankuna. Akwai kashe-kashe da yawa da kara sace-sace da ke faruwa a Arewa, musamman ma yankunan da aka ambata a sama wadanda ba a ba da rahoto ba.

“Wasu lokuta ana kashe wadanda aka sace, wasu kuma a sanya su kan aikin karfi na dindindin, mata kuma akan yi masu fyade da karfi daga wadanda suka sace su. Mafi yawan wadanda abin ya shafa ana kama su ne a gonakinsu na noma yayin gudanar da ayyukansu na yau da kullum da suka dage da yi domin biyan bukatun iyalansu.

“Har wala yau, sabon karin farashin kayayyakin masarufi, musamman kayan abinci a kasuwannin Nijeriya, bai zo mana da mamaki ba, duba da yadda alaka ta kasance tsakanin rashin tsaro da karancin abinci. Yanayin rashin taimako, wanda mutanenmu suka samu kansu a ciki, ya sanya su yin watsi da harkokinsu na noma, don haka ya haifar da karancin abinci a kasar a halin yanzu,” in ji sanarwar.

Bugu da kari, dattawan sun ce “Bayanin da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta yi a ranar Litinin din da ta gabata na cewa hauhawar farashin kayayyaki a kasar nan ya haura zuwa kashi 14.23 bisa dari (na shekara-shekara) a watan Oktoba, wanda ke nuna karuwar kashi 0,52, bai zo mana da mamaki ba. Muna tunawa tare da nadamar cewa hauhawar farashin kayayyaki a kasar nan a yanzu ya haura zuwa wannan matakin sama da 13.71 a watan Satumba.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Farashin masu Sayayya (CPI), lissafi wanda ke auna matsakaicin farashin kayayyaki da aiyukan da mutane ke yi a kan lokaci, wanda hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar, ya nuna cewa adadin ya kuma karu da kashi 1.54 a kowane wata idan aka kwatanta da kashi 1.48 bisa dari da aka samu a watan Satumba.”

“Mun san muna shiga wannan yanayin na karancin abincin kuma mun dade muna fadakar da hukumomin da suka dace kan hanyoyin da za a bi don magance hakan, daya daga cikinsu shi ne kiran da muke yi ga gwamnatin tarayya, karkashin jagorancin Shugaba Muhammad Buhari ta sake fasalin tsaro, don samun ingantaccen aiki ta yadda manoma za su iya komawa yankunansu na gona. Zamu ci gaba da gabatar da kiraye-kiraye don ganin an samar da isasshen tsaro ga mutanenmu na Arewa, don magance matsalar karancin abinci da ake fama da ita a yanzu, wacce ta kai ga hauhawar farashin kayan masarufi zuwa wani matsayi, domin idan ba haka ba abin zai kara munana,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta karkare da cewa, “Tsoronmu shi ne, idan ba a yi wani abu cikin gaggawa don sake fasalin tsarin tsaro a kasar nan ba, yanayin talauci na iya kara muni, tare da haifar da mummunan sakamako a kan halin da ake ciki na rashin tsaro.”

Exit mobile version