A kwanakin baya ne Babbar Kotun Jihar Legas ta aiwatar da hukunci cewa kudaden da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Tu’annuti da Kudaden kasa EFCC ta damke a banki mallakin Tsohuwar Ministar Man Fetir, Madam Diezani Alison-Maduake kimanin naira bilyan 35 ba halastattu ba ne.
Tun da farko hukumar ta EFCC ta bayyana cewa tsohuwar ministar ta sace kudaden ne daga asusun Hukumar NNPC a lokacin da ta ke shugabantar ma’aikatar, sannan ta adana su a bankunan Nijeriya daban-daban. A dalilin wannan zargi ne EFCC ta maka Diezani kotu inda aka samu wannan hukunci.
Haka kuma a wannan shafi, mun yi magana kan irin wannan batun cewa wasu ‘Yan Nijeriya na satar kudaden da ba su da bukatar su sam-sam, haka kuma irin wannan sakamako da ake samu daga wasu kotuna da dada yin nuni bisa irin munin almundahanar da wasu shugabanni suka tafka. Lamarin kuma har ila yau ke bayyana ‘yan Nijeriyar da suka kade hannunwan su wajen gyara tare da dora Nijeriya bisa turba nagari ta yadda ‘yan baya za su amfana.
Yanzu irin wadannan makudan kudade ma’aikatu da hukumomin gwamnati nawa ne a kasar nan ke samun irin su a matsayin kasafin shekara? Amma abin takaici sai ka iske daidaikun shugabanni na wawashe taskokin dukiyar kasar da aka damka musu amanar ta don amfanin milyoyin al’umma saboda tsabar son zuciya da rashin kishin kasa.
Sannan idan wannan hukuma ta ci cigaba da tsananta aiwatar da irin wannan bincike, to akwai tabbacin za ta sake bankado ko gano halin beran da marasa kishin kasar nan suka tafka a lokacin da al’ummar Nijeriya ke tsananin bukatar dukiyar.
Kafin haka fa akwai makudan kudi har dalar Amurka bilyan biyu na makamai da aka karkatar don gudanar da yakin neman zaben tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a 2015. Haka zalika Allah ne kadai masani ga ire-iren badakalar kudaden da shugabannin hukumomi suka danne a yayin da suke kan madafun iko!
Har ila yau, wani abin dubawa game da wannan hukunci shi ne, ‘yan Nijeriya na bukatar ganin an hukunta irin wadannan shugabannin don ya zamo darasi ga na baya. Barayin gwamnati sun dade suna aiwatar da tu’annuti da dukiyar kasa ir- daban-daban tare da hadin bakin bankuna ana boyewa da kuma fitar da kudaden zuwa kasashen ketare cikin sauki.
Sannan abu ne sananne ga dukkaninmu cewa wannan gwamnatin ta Muhammadu Buhari ta mayar da hankalinta ne dungum wajen tsamo ko fitar da Nijeriya daga halin faduwar tattalin arziki wanda ke yi wa kasar barazanar durkushewa, sannan tana muradin samun kudaden da aka wawashe din cikin gaggawa don ci gaba da ceton kasar daga halin da ta samu kanta.
Sai dai gwamnatin na takaita ida hukuncin wanda aka samu da laifin al’mundahanar muddin dai an samu kadaden da aka sacen, lamarin kuma ba zai haifar da da mai ido ba ga kasar, amma kwato kudaden sannan kuma da hukunta mai laifin a lokaci guda yana isar da sako ne zuwa ga masu irin wannan halin.
Wani karin abin takaicin shi ne yadda suka kwashe madarar kudaden ba kadara ba. Kari kan haka kuma ya hada da hatta jami’an tsaron kasar nan na cikin wannan badakala dumu-dumu wajen bada kariya ga ire-iren wadannan shugabannin har su cimma burin su na kassara kasar! Don haka dole ne su ma su fuskanci shari’a don dandana kudar sakamakon ayyukansu.
Bugu da kari, hatta bankuna akwai ayoyin tambaya masu tarin yawa akan su bisa rashin ingancin su ta hanyar taimakawa masu al-mundahanar suna samun damar tserewa da kudaden zuwa kasashen ketare cikin sauki. Don haka su ma ya kamata su fuskanci shari’a.
Saboda haka muna kira ga Gwamnatin Tarayya cewa ta runtse ido wajen hukunta dukkan masu hannu cikin wannan badakalar cikin gaggawa, sannan a rika kwace lasisin hada-hadar da suke da wadannan kudaden. Kuma babu ko shakka cewa wannan hukunci da kotu ta yanke akan tsohuwar ministar, sako ne a zahiri dake zuwa ga azzaluman kasar nan cewa irin wancan lokaci na yin wasoso da dukiyar al’umma ya wuce sannan duk wani wanda ya aikata irin wannan ta’adi ba zai kai labari ba, ta hanyar fuskantar hukunci mai tsanani.