Daga Ibrahim Muhammad,
Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli na jihar Kano Alhaji Abdullahi Ma’azu Gwarzo Baban Gandu ya yaba wa Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC saboda tsara abubuwa da tabbatar da gudanar zabe na kananan hukumomi a jihar Kano da jam’iyyar APC ta yi nasara.
Ya ce su a Gwarzo an kai Mayan zabe da wuri kuma wakilan jam’iyyu sun shaida anyi zabe a dukkan mazabu al’umma sun fito suka sake zabar shugaban karamar hukumar Gwarzo domin ya zarce a karo na Biyu wannan ya nuna yana zaman lafiya da jama’a kuma sun gamsu da mulkinsa na farko bisa yanda aka kada masa kuri’u a Gwarzo.
Ya ce abin da ya jawowa shugaban karamar hukumar nasarar, shi ne zama lafiya da al”umma da irin ayyuka da Gwamnatin APC take tun daga matakin kasa jiha, karamar hukumar da mazabu duk dan siyasa a wannan yanayi da ake ciki dole ya yi wa Allah godiya da jagorori da aka samu a wannan yanayi musamman in aka kalli karamar hukumar Gwarzo kusan dukkaninsu da Gwamnan Kano ya basu madafun iko duk matasa ne.
Alhaji Abdullahi Mu’azu Gwarzo ya yi kira ga al’umma musamman masu mulki a Gwarzo dana sauran madafu musamman shugaban karamar hukuma da kansiloli da aka zaba su sani nauyi ne Allah ya dora musu kuma kamar yau aka taru aka zabesu kuma idan wa’adinsu ya yi za su sauka in kaje ofishin shugaban karamar hukuma zaka ga sunaye wajen 40 wane ya yi ya sauka wane ma haka kaima wata rana za a zo kanka ka sauka to dole ne abinda zaka rika tunawa me kayi a baya kuma dukkanin kulawa da tsaro shugaban karamar hukuma Gwarzo yana iya kokarinsa kwarai da gaske, dole a yaba masa, wannan abubuwa yakamata duk.wani shugaba ya tuna Allah zai tambaye su ranar alkiyama hakkunan al’umma dan haka su rike amana.