Daga Bashir Ahmad
Shugaba Muhammadu Buhari a yau ya gana da shugabannin rundunonin tsaro na kasa a ofishinsa a fadar Aso Rock Villa a Abuja.
Wannan ganawa ta biyo bayan gargadin da Shugaba Buhari ya yi a jiya cikin jawabinsa ga ‘yan kasa na cewa jami’an su tabbatar tare da daukar duk matakan da suka dace kan duk masu yunkurin kawo barazana ga dorewar dunkulalliyar Nigeria.
Haka a cikin jawabin na sa a jiya, Shugaba Buhari ya kuma nemi shugabannin tsaron na kasa da su kara tsage dantse da kaimi wajen kawo karshen kungiyar Boko Haram, da dakile mummunar dabi’ar satar mutane da sauran laifuka makamantan hakan.