Ganduje Bashi Da Hannu A Zanga-zangar Da Muka Yi A Kaduna – NLC

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

kungiyar kwadago ta kasa ta musanta zargin da ta ce Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufai ya yi na cewa Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne ya bai wa kungiyar kudi domin su yi masa zanga-zanga a Kaduna.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar kwadagon ta kasa Kwamared Ayuba Wabba, ya ce Ganduje ba shi da hannu ta kowacce fuska a kan zanga-zangar da suka gudanar.

Sanarwar ta ce kungiyar ta gudanar da zanga-zangar ce kawai saboda yadda Gwamna Nasir wl-Rufai yake cisguna wa ma’aikata a Jihar Kaduna da kuma yadda yake korarsu daga aiki ba gaira babu dalili.

“Mun ci karo da wani faifan bidiyo da ya nuna Gwamna Nasir el-Rufai yana zargin Ganduje da ba mu kudi domin mu yi zanga-zanga, Ina so el-Rufai ya sani kungiyarmu ba ta yarda wani ya shigo cikinta har ya ba mu kudi don mu yi wani abu”. In ji Wabba

Sanarwa ta yi kira ga jama’an tsaro da su sanya idanu domin gudanar da aikin su yadda ya dace saboda yadda el-Rufa’i yake yi wa ma’aikata da kungiyar kwadago barazana, inda yace barazanarsa ba zata hana kungiyar neman hakkin ‘ya’yanta ba.

Daga karshe Ayuba Wabba a cikin sanarwar ya ce kungiyarsu kowa ya santa da dattako wajen gudanar da aiyukanta a kan tsari, ya ce zasu tabbatar da ganin sun ci gaba da kasancewa a kan wannan matsayi domin kare martaba da mutuncin ma’aikata a kasar nan.

Exit mobile version