Abdullahi Muhammad Sheka">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home SIYASA

Ganduje Ne Kadai Ya Kammala Shirin Fatattakar Cutar Covid-19 –Fatima Dala

by Abdullahi Muhammad Sheka
March 31, 2020
in SIYASA
5 min read
Ganduje Ne Kadai Ya Kammala Shirin Fatattakar Cutar Covid-19 –Fatima Dala
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

HAJIYA FATIMA ABDULLAHI DALA, Mashawarciya ce ta musamman ga Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin inganta rayuwar mata da yara, kuma guda cikin Shuhada’un Gwamna Ganduje, gogaggiyar ‘yar gwagwarmaya ta fuskar kyautata harkokin mata da yara. A tattaunawarta da Wakilin LEADERSHIP A YAU a Jihar Kano, ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, Hajiya Fatima Abdullahi Dala ta bayyan kyakkyawan fatan da al’ummar jihar ke da shi kan aniyar Gwamna Gaduje, Sannan kuma ta yi tsokaci kan aniyar Gwamna da kuma jaijircewarsa, domin dakile yadauwar matsalar cutar Cobiv-19, wadda a halin yanzu ke addabar duniya baki-daya. Ga dai yadda tattaunawar tasu kasance:

 

samndaads

Kasancewarki mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin mata da yara a Jihar Kano, a wannan lokaci an gamu da matsalar da ta yi sanadiyyar rufe makarantu, ko yaya kike kallon wannan hali da aka tsinci kai a ciki?

Gaskiya ne, kamar yadda aka sani ita wannan matsala ba Jihar Kano ko Nijeriya kadai ke fama da ita ba, matsalar cutar Coranabirus annoba ce wadda Allah Ya kaddarawa duniya ita, al’amari ne da ya shafi duniya baki-daya. Kuma Alhamdulillahi, jajirctaccen Gwamna wanda Kanawa ke alfahari da shi, shi ne Gwamna daya tilo, wanda ya zarta sauran ta fuksar kokarin kare hakkin yara da mata. Wannan tasa daga bullar wannan cuta, Gwamna Ganduje bai iya rutsawa ba domin hankalinsa na kan yara da mata.

Wadanne abubuwa Gwamnan ya yi har da kike ganin ya zarta tsararsa sauran Gwamnonin Jihohi Nijeriya?

An zo wurin, ba na jin kuna da lokacin da za ku iya bayarwa domin yi wa kokarin Gwamna Ganduje dalla-dalla, amma dai idan aka duba tunda farko jin bullar cutar da kuma yadda ake kamuwa da ita, yasa Gwamna Ganduje bayar da umarnin fara rufe makarantu a fadin Jihar Kano baki-daya, wanda hakan ke tabbatar da tsanani kishin Gwamnan ga cigaban al’ummar da yake wakilta. Sannan kuma, baya ga haka sai da Gwamnan ya tabbtar da samar da ingantattun matakan tunkarar wannan matsala, inda ya kafa wani kwakkwaran Kwamiti, karkashin Mataimakinsa Dakta Nasiru Yusif Gawuna, wanda ke Shugabantar Kwamitin. Muna kara yi wa Allah godiya da samun gogaggen jagora ganin irin kulawar da Gwamnan ke yi wa Kanawa.

 

Tunda ba akan yara kadai kike baiwa Gwamna Ganduje shawara ba, har da harkokin inganta rayuwar mata, shin a wancan bangare kuma me za ki iya bugar kirji da cewa, Gwamnan ya yi wa matan Jihar Kano?

Ina tabbatar maka da cewa, ko hasidin iza hasada ne ya kalli irin hidimar Gwamna ke yi wa harkokin mata a Jihar Kano, zai aminta da cewa tamu ba irin tasu ba ce. Da farko, a wancan zangon wannan Ofis din yara kadai aka damka amanar bayar da shawawara a kai, amma ganin jajircewa da kuma kokarin rike amanar da Gwamna ya damka a hannuna, yasa a wannan zangon aka fadada aikin Ofis aka hada da harkokin inganta rayuwar mata.

Mu kamar ma gani muke yi mu kadai mata Gwamna Ganduje ya fi hidimtawa, domin tunda ake Gwamnati a Jihar Kano, ba a tabayin Gwamnatin da ta shigar da mata cikin kunshin gwamnati ba, kamar Ganduje. Yanzu haka, dubi yawan Kwamishinoni mata, manyan Daraktoci, Sakatarori, Mashawarta, Mataimaka na musamman, wadanda duk suke cikin wannan gwamnati. Sannan kuma, ga tsarin Gwamna Ganduje na samar wa da mata sana’o’in dogaro da kawunansu.

Wannan ko shakka  babu, an yi ittifaki yanzu haka Gwamna Ganduje shi ne wanda ya bujiro da hanyoyin da ake koyawa mata sana’o’i iri daban daban, musamman batun horar da matan aikin gyaran mota wadda aka tura sama da mata 200 zuwa Kamfanin Peugeot da ke Kaduna, inda suka samu ingantaccen horo, wanda a halin yanzu akwai adadin mata masu yawa da suka bude wuraren gyaran motci irin na zamani, sannan kuma Gwamnan bayan horar da matan da aka yi, ya yi musu goma ta arziki wajen saya musu kayan aiki tare da ba su jari.

Shin zuwa yanzu wadannan ayyuka ofiishin naki ya fi mayar da hankali a kansu?

Akwai abubuwa masu yawa da ke kunshe a cikin wannan Ofis, daga ciki akwai tsarin da muke yi na ganawa tare da tattaunawa kan matsalolinsu, kasan ita mace a lokuta daban-daban, babban abinda ta fi bukata shi ne a saurare ta domin jin matsalarta, a wani lokacin abinda suke bukata bai wuce jari ba, wasu kuma batun tallafin karatu suke nema, yayin da wasu kuma ke bukatar samun aikin yi, wanda hakan tasa Gwamnatin Ganduje samar da tsarin sama wa mata damar shiga makarantu daban-daban.

Wani abin sha’awa ga dukkanin wanda ya halarci bikin kaddamar da aikin gadar sama, wadda ta fara daga Asibitin Murtala ta wuce har zuwa titin Ibrahim Taiwo, wanda a lokacin kaddamar da wannan aiki ne aka ga fuskokin mata Injiniyoyi wanda suka samu horo kan irin aiki, wanda a baya ake zaton maza ne kadai ke iya yin wannan aiki. Wannan ya kara wa Gwamnatin Jihar Kano kima kwarai da gaske.

 

Cutar Covid-19 ce ke zama babbar matsalar da ake ta faman cece-kuce a kanta, shin me za ki ce dangane da yunkurin magance matsalar?

Ai Gwamna tuni ya gama tattara makaman murkushe wannan matsala baki-daya da yardar Allah, domin da farko dai Gwamna Ganduje a ranar Litinin da ta gabata sai da ya yi wa al’ummar Jihar Kano jawabi, inda ya jajantawa jama’a halin da aka samu akai a ciki, sannan kuma ya bayyana wasu matakai da gwamnati ta dauka domin magance matsalar, wadanda suka hada da rufe makarantu, tattaunawa da Sarakuna, Malamai da kuma sauran Shugabannin al’umma domin duba matsayar da ya kamata a dauka ta fuskar batun kauracewa shiga cinkin cinkoson al’umma.

Haka kuma, Gwamna Ganduje ya bayar da umarnin rufe dukkanin gidajen da ake
gudanar da tarukan bukukuwa, wanda ke tara al’umma masu yawa a lokaci guda, sannan Gwamna ya bukaci Sarakunan Kano baki-daya, da su koma yankunansu domin tattaunawa da Malamai domin cigaba da gudanar da addu’o’in fatan kawo karshen wannan matsala. Kuma Alhamdulillahi, har zuwa wannan lokaci ba a samu bullar cutar a Kano ba.

 

Tunda kuke tare da mata da kuma yara, shin wace shawara za ki bayar domin kaucewa shiga cikin cunkoso, wanda ake ganin yana cikin hanyoyin da ake kamuwa da wannan cutar?

Alhamdulillahi, a wannan gaba tuni mai girma Gwamna ya gama komai, sai dai kawai abinda ake fata ga al’umma cigaba da yin addu’a tare da bin dokokin da aka gindaya, wanda ake ganin suna cikin hanyoyin kaucewa yaduwar wannan cuta.

Sannan akwai bukata iyaye su lura kwarai dangane da wuraren da suke shiga, domin Gwamna saboda kishin yara ya bayar da umarnin rufe makarantu, domin killace yara a cikin gidajensu, to amma har yanzu iyaye na kewayawa wurare daban-daban, wannan tasa nake kara baiwa iyaye shawarar lura da dukkanin wuraren da suke shiga, sannan su kuma lura da ire-iren mutanen da za su yi mu’amala da su zuwa dan lokacin da aka bayar domin dakile yaduwar matsalar.

Sannan kuma, ina kara kira gare mu wadanda Gwamna ya damka amanar wani bangare na ayyukan da suka rataya a wuyansa a hannunmu, domin rikewa Gwamna masoya tare da kyautatawa ‘yan Jam’iyya, hakan ko shakka babu zai kara hasken fitilar wannan Gwamnati, domin cigaba da kwararawa Kano da Kanawa ayyukan alhairi.

A karshe, ina kara mika godiya ta musamman ga mai girma Gwamna, bisa kyakkyawar kulawar da ake baiwa harkokin yara da mata a Jihar Kano, wannan Allah shaida ne al’ummar Kano sun yi sa’ar jagora bisa irin hobbasan da a ke yi wajen kyautata rayuwar al’ummar Jihar Kano.

 

Mun gode.

SendShareTweetShare
Previous Post

Dole Manoma Su Rungumi Noman Rani, Cewar Kwararre

Next Post

Muhimmancin Tsafatace Muhalli

RelatedPosts

Har Yanzu Sakkwatawa Ba Su Fara Morar Dimukradiyya Karkashin Mulkin Tambuwal Ba – Umar Lili

Har Yanzu Sakkwatawa Ba Su Fara Morar Dimukradiyya Karkashin Mulkin Tambuwal Ba – Umar Lili

by Abdullahi Muhammad Sheka
4 months ago
0

Shugaban kungiyar matasan jihar Sokoto kuma dan gwagwarmayar ganin an...

Wane Ne Hon. Mal Samaila Suleiman (Dujiman Zazzau)?

Wane Ne Hon. Mal Samaila Suleiman (Dujiman Zazzau)?

by Abdullahi Muhammad Sheka
7 months ago
0

Hon. Malam Sama'ila Sulaiman (Dujiman Zazzau) an haifeshi ranar 03/02/1981,...

Bala Abu Ga Sanata Mandiya: Babu Taimakon Da Ka Yi Wa ‘Yan Gudun Hijirar Faskari

Bala Abu Ga Sanata Mandiya: Babu Taimakon Da Ka Yi Wa ‘Yan Gudun Hijirar Faskari

by Abdullahi Muhammad Sheka
7 months ago
0

Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC yankin Funtua a jihar Katsina, Alhaji...

Next Post
Muhimmancin Tsafatace Muhalli

Muhimmancin Tsafatace Muhalli

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version