Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da Sabon zangon karatu na Shekara ta 2020/2021 na makarantun sakandire da firamare naGwamnati da masu zaman kansu a Jihar Kano.
Don Haka Gwamna Ganduje ya bada umarnin bude makarantun a ranar 18 ga watanni Janairun shekara ta 2021. Kamar yadda Kwamishinan Ma’aikatar ilimin na Jihar Kano Malam Sanusi Muhammad Kiru ya shaidawa manema lambarai a ranar Juma’ar data gabata a Kano.
Idan za’a tuna Gwamnatin Jihar Kano ta bada umarnin rufe makarantun ne tun a ranar 15 ga watan disambar Shekara ta 2020 sakamakon garkuwa da dalibai sama da 300 a Jihar Katsina da kuma sake dawowar annobar Korona.