Ganduje Ya Bada Umarnin Bude Makarantun Firamare Da Sakandire

Hukumar

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da Sabon zangon karatu na Shekara ta 2020/2021 na makarantun sakandire da firamare naGwamnati da masu zaman kansu a Jihar Kano.

Don Haka Gwamna Ganduje ya  bada umarnin bude makarantun a ranar 18 ga watanni Janairun shekara ta 2021. Kamar yadda Kwamishinan Ma’aikatar ilimin na Jihar Kano Malam Sanusi Muhammad Kiru ya shaidawa manema lambarai a ranar Juma’ar data gabata a Kano.

Idan za’a tuna  Gwamnatin Jihar Kano ta bada umarnin rufe makarantun ne tun a ranar 15 ga watan disambar Shekara ta 2020 sakamakon garkuwa da dalibai sama da 300 a Jihar Katsina da kuma sake dawowar annobar Korona.

Sanarwar ta nuna Umarnin Gwamna cewa Dalibai dake makarantun kwana zasu koma makarantun sur tun a ranar 17 ga watan Janairun Shekara ta 2021.

Exit mobile version