Abdullahi Muhammad Sheka" />

Ganduje Ya Bukaci Karin Mutum 88,000 Domin Amfana Da Tallafin GEEP A Jihar Kano

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci Ma’aikatar jinkai,  harkokin annoba da Cigaban al’umma  domin su amince dad a karin akalla mutane 2,000 da zasu amfana da wannan tallafi daga kananan Hukumomi Jihar Kano 44 cikin shirin tallafin Gwamnatn Tarayy na (GEEP).

“Kasancewar  Jihar Kano ce keda  yawan al’umma a fadin kasarnan tana bukatar samun karin mutum 88.000 da ya kamata su amfana da shirin tallafin kasuwanci na (Trader Moni) da tallafin Manoma a zagayen shirin  na gaba.”
Gwamnan wanda mataimakinsa Dakta Nasiru Yusif Gawuna  ya wakilta ne ya bayyana haka alokacin kaddamar da shirin raba tallafin kudi  ga matan karkara da aka gudanar a fadar Gwamnatin Jihar Kano ranar Litinin.
Ganduje ya nuna cewa, Jihar Kano ke da yawan adadin mutane dubu 200,000 da suka yi rijista da shirin N-power a fadin kasar nan, don haka sai ya bukaci ma’aikatar jinkan da suyi amfani da damar da suke da ita wajen samarwa Jihar Kano karin adadin wadanda zasu amfana nan gaba.
Da ya ke mika sakon farin cikin su bisa karin wadanda zasu amfana na adadin mutane 35,000 na shirin musayar kudi daga kananan Hukumomin Jihar Kano 15, don haka sai ya bukaci gaggauta amincewa da shigar da sauran mutane dubu 35,000 daga kowacce karamar Hukuma. Haka kuma Gwamnan ya jinjinawa kokari da jajircewar Gwamnatin Tarayya  bisa kyawawan manufofi da ake aiwatarwa wanda suke  daga daraja da kuma inganta rayuwar matan karkara.
Da ya ke jawabi tun da farko Ministar ma’aikatar jinkai da cigaban al’umma Hajiya Sadiya Umar Farouk wadda babban sakataren hukumar  Alhaji Bashir Nura Alkali wanda yace tallafin Naira dubu 20,000.00 ga sama da mata 125,000 a fadin kasarnan ta karkashin shirin inganta rayuwar matan karkara wanda aka tsara a shekarar data gabata domin inganta rayuwar mata na Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
“Fatanmu a Jihar Kano shi ne raba wannan tallafi ga mata dubu 8,000 a fadin kananan Hukumomin Jihar Kano 44. Ana sa ran tallafin ya habaka harkokin kudaden shiga da kuma zama masu dogaro da kansu. Don haka sai ya bukaci  wadanda suka amfana da wannan tallafi suyi amfani da shi wajen inganta rayuwarsu,” in ji Ministan.

Exit mobile version