Ganduje Ya Gode Wa Jama’ar Kano Bisa Nasarar Mika Wa Sarki Sandar Girma

Ganduje


Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Domin nuna goyon baya da karfafa guiwa ga sabon Sarkin na Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, Shugaban kasa Muhannadu Buhari, Wanda  mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya wakilta, ya godewa Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, inda ya nuna nadin Sarkin da bashi sandar kama aikin da cewa gagarumin sauyi ne.

Farfesa Osinbajo ya bayyana haka ne alokacin bikin mika sandar ga Sarkin Kano Aminu Bayero, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha a ranar asabar. “Mai girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje Ina taya ka murna a wannan lokacin da ka samar da wannan gagarumin sauyi na rantsarwa tare da mikawa Sarkin shaidar kama aiki ga Mai Martaba Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero.”

Yace, ” a gare ni wannan abin alfahari ne kasancewa ta a wannan birni mai cikakken tarihin al’adu inda na wakilci Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin shaida wannan gagarumin taro na mikawa Alhaji Aminu Ado Bayero sandar girma a matsayin Sarki na 15 a Daular Fulani.”

“Mai martaba Sarki  ba sai an bayyana cewa birnin Kano ba irin sauran birane bane ta fuskar tarihi a irin wannan lokacin. Kano ako da yaushe ta kasance cibiyar Kasuwanci da tattalin arziki a fadin afrika. Sannan kuma masauki ne na kabilu daban daban da al’adu daban daban.

Ya ci gaba da bayyana farin cikin cewa, ” Zama da dukkan kabilun lafiya tare da kiyaye al’adun Kano ta hakan aka samu dorewar zaman lafiya. Ta Hakan za’a tabbatar tsarin Kasuwanci da tattalin arziki, haka kuma akwai masu dukiya amma duk da haka ba’a barta abaya ba ta fuskar kyakkawan tsarin siyasa.

Ya kara da cewa, “Kano birni ne na Mutumin  kirki mutun na talakawansa, Malam Aminu Kano da sauran mutanen arziki masu da’a. Haka kuma Kano gidane na attajirin nan na afrika, Alhaji Aliko Dangote. Daga duk inda kazo, kamar kana gidanka ne.

A cikin wasikar da Shugaban kasa Buhari ya aikawa da Sarkin,  wadda Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, wanda kuma ya kasance baffa ne ga Sarkin, Shugaban kasar yace, ” Ina mika sakon taya murna gareka bisa nasarar gadon mahaifinka, a matsayin Sarki na 15 daga Daular Fulani, daga bangaren Sullubawa, Hakan  abin  jinjinawa da cancatar wannan nadi da aka gudanar ranar Asabar 3 ga watan July, shekara tà 2021.

Wasikar ta ci gaba da cewa, nadin ka da baka sandar kama aiki ya cancanta, kasancewar lamarin ya Faru cikin tarihin kasarmu ya yinda ake fuskantar yanayin siyasa ke farfadowa ta hannun aminimmu, mahaifinka Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, Allah ya jikansa da gafara,”

“Kamar yadda nake ci gaba da yi maka addu’ar samun nasara, muna bukatar gudunmawar ka domin daga darajar al’ummar masarautar Kano da kasa Baki daya. Ina son tabbatar maka da goyon bayanmu domin barin kyakkyawan tarihi,”

Da yake mika godiyarsa, Gwamna Ganduje yace ” dukkanin Sarakunan da Suka hadu a wannan wuri,  musamman Mai alfarma Sarkin Musulmi, ya mutuntamu kwarai da gaske, kasancewarsa a wannan wuri.  Rabanmu da irin wannan tun lokacin da muka halarci irin wannan irin muhimmin taro, a lokacin Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, lokacin da yake mika ragamar aiki.”

“Ba tare da wani kokonton ba, wannan bukukuwan har zuwa wanda ake yanzu  Jama’ar Kano sun karbi wannan biki. Wannan tasa duk inda ka shiga  a Kano Yau Jama’a na murna sakamakon wannan biki. Wanda hakan ke nuna yadda Mutane suka karbi wannan biki mai tarihi.

Kowa da kowa kama daga Shugabannin addini, matasa maza da Mata, ‘yan Kasuwa daga kowane bangare na al’umma ciki harda ‘yan uwa na jini a masarautar duk sun gamsu da wannan Sarki. Inji shi

Gwamna Ganduje yace “Mai Martaba Muna matukar farin ciki da yadda kake jagorantar wannan Masarauta. Muna ganin yadda kake taimakawa Gwamnati ta hanyoyin ci gaba masu yawa. Muna farin ciki da haka.  Muna rokon Allah ya ci gaba da kiyaye ka tare da Yi maka jagora.”

Da yake kara nuna gamsuwarsa cewa ya yi,  Babu kokonton cewa Marigayi Ado Bayero wanda ya yi jagoranci sama da Shekara 50, ya inganta zaman da kwanciyar hankali a Jihar Kano.

Ya kara da cewa,  “Ya yi aiki da Gwamnoni da yawa a Jihar Kano. Ya Yi aiki da Gwamnonin Mulkin soja da fararen hula. Haka Kuma ya kara yin aiki da Wasu Gwamnonin na soja.

Daga Shekara tà 1998 ya yi aiki da Gwamnonin farar hula. Alokacin ba’a samu wata matsàla tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Masarauta ba.”

Ya ci gaba da cewa,  wannan wani kyakkyawan ci gaba ne inda Sarkin ya gaji mahaifinsa, ”  tun lokacin da aka zabeshi ya ciga da  dorawa a inda mahaifinsa ya tsaya wajen kokarin sada zumuncin tsakanin masarautar Kano da sauran Masarautun kasarnan.

Yana girmama su yadda ya kamata a fadarsu.  Hakan ce tasa suke sakawa da alhairi. Wannan tasa muka gamsu duk sun hallara a wannan wuri.”

Sama da Sarakuna 100 ne na fadin Kasarnan da sauran Kasashen duniya suka halarci wannan biki. Da yawa sunzo daga shiyyoyin shida na kasarnan.

Haka kuma akwai Gwamnoni 8 daga sassan kasarnan da suka zo wannan taro da kansu wanda suka hada da Gwamnonin Jigawa, Katsina, Zamfara, Kebbi, Sokoto, Bauchi, Kogi da Legas.

Shugaban Majalisar dattijai, Dakta Ahmad Lawan da sauran Shugabannin Majalisar dattijai tare da ‘yan Majalisar wakilai ta Tarayya suma sun halarci Bikin.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Mai alfarma Sarkin Musulmi Dakta Muhammad Sa’ad Abubukar, Shehun Borno, Ooni na Ife Adeyeye Enitan Ogunwusi, Mai daraja Oba na Benin, Omo N’oba Ewuare III, Mai daraja Ooni na Oni da Mai Martaba Sarkin Gwandu da sauransu.

Akwai Sarakuna da yawa daga Kasar Senegal, Tarayyar Chadi, Cameroon, Niger da Jakadu daga Afrika ta Kudu, Indiya da sauran Kasashen duniya da suka halarci taron.

Minustoci kasarnan suma sun halarci bikin, tare da Shugabannin sassan ma’aikatun Gwamnatin Tarayya. Kamar yadda babban Daraktan yada labaran Gwamnan Jihar Kano Abba Anwar ya Shaidawa LEADERSHIP A Yau.

Exit mobile version