Ganduje Ya Janyo Ra’ayin Masu Zuba Jari A Kano Daga Waje Ta Hanyar Ba Su Filaye Kyauta

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce, Jihar na shi na bukatar masu zuba jari daga waje a mahimman sassa kamar na sashen samar da hasken lantarki, Noma, Manyan ayyuka da tonon  albarkatun kasa, domin ta habaka tattalin arzikinta.

A cikin wani bayani da babban darakta, kan yada labarai na gidan gwamnati, Ameen Yassar, ya fitar, gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin taron shekara-shekara na 8 kan zuba jari, da ake yi a Dubai.

Yassar ya ce, gwamnan ya ce, gwamnatin sa za ta bayar da tallafin ma’aikata da kuma shirya yanda za a rika sauya kudaden riba, duk da yanda ya nu na gwamnatin na shi ba ta amince da cin hanci da rashawa ba sam.

“Gwamnati na, ta mika gayyata ga masu zuba jari daga waje, kan shiri na musamman, za kuma ta ba su bukatun su na musamman kamar filayen kafa masana’antu, saukake masu haraji, samar masu da manyan ayyuka na musamman da kuma tabbatar ma su da lafiyayyun wurare.”

“Gwamna Ganduje ya ce, “Bankin Duniya ya kiyasta Jihar Kano a matsayin lafiyayyen wajen yin harkokin kasuwanci a matsayi na 23, (a 2017), Jiharmu ta kara mayar da himma wajen nu na kauna ga masu zuba jari.

“Wani babban kamfani na kasar China mai suna, ‘Shandong Ruyi Technology,,’ har ya ci moriyar garabasar namu ta saukake hanyoyin zuba jarin, a yanzun haka ya zuba jarin sama da dala milyan 600, wajen kafa masaka da kamfanin yin tufafi a Kano.

“Gwamna Ganduje, ya gana da Sakataren ma’aikatar tattalin arziki na daular larabawan ta tsakiya, Abdullah al-Saleh, inda suka tattauna kan yiwuwar hada hannu a sashen noma.

“Gwamnan kuma, tare da takwaran sa na Jamhuriyar Nijar, Abubakar Bello, sun tattauna da wani babban jami’i na gidan sarautan na Dubai, kuma mamallakin rukunin kamfanonin nan na AMERI, Sheikh Ahmad bin Dalmook Al-Maktoum, kan yiwuwar zuba jarin.

“Ya shaidawa gwamnan cewa, rukunin kamfanonin na shi na AMERI, ya sanya hannu kan takardan fahimtan juna da gwamnatin Jihar Legas, kan wasu sassa, ya kuma gina tashar samar da hasken lantarki a Ghana, wacce za ta haskaka wasu Jihohin kasar.”

Taron masu zuba jarin na shekara-shekara, shi ne taron masu zuba jari ma fi girma na duniya inda kai tsaye masu zuba jarin kan tattauna da junansu.

 

Exit mobile version