Sakamakon zabar Gawuna da gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi a matsayin wanda zai wa Jam’iyyar APC takarar gwamnan Kano a zaben 2023.
Zabar Gawuna ya sanya wasu ‘yan takara da dama sun gaza kai bantensu na fatan da suke da shi na gadon kujerar gwamnan Kano daga hannun Ganduje. Ciki harda Inuwa Waya da A.A Zaura.
- 2023: Ganduje Ya Zabi Mataimakinsa Gawuna A Matsayin Wanda Zai Gaji Kujerarsa
- 2023: Lokaci Ne Kadai Zai Tabbatar Da Matsayarmu Kan Takara – Gawuna
Labarai24 ta rawaito cewa, Abdulsalam Abdulkarim Zaura da aka fi sani da A.A Zaura da kuma Malam Inuwa Ibrahim Waya na daga cikin waɗanda ke son jam’iyyar APC ta tsayar da su takarar gwamnan jihar ta Kano a zaɓen 2023, sai dai kuma da alama burinsu na neman zama tarihi.
A.A Zaura wanda shi ne ake ganin yana ɗaukar nauyin jam’iyyar wajen hidimomin da su ka shafi kashe mata kuɗaɗe da kuma taimakon ƴan jam’iyyar ya gaza samun goyon bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa dalilan rashin ƙwarewa a harkokin mulki da kuma tuhumar da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa, EFCC ta ke masa na aikata laifin damfarar miliyoyin kuɗaɗe.
Shi kuwa Inuwa Ibrahim Waya wanda tsohon darakta ne a kamfanin mai na Najeriya, NNPC, ya haɗu da cikas ne wajen samun goyon bayan Ganduje bisa jita – jitar da ake yadawa akan baiwa gwamnan maƙudan kuɗaɗe akan ya ba shi takarar gwamnan.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa Gwamna Ganduje ya yi fushi sosai akan wannan jita – jitar inda ta kai ga ya gayyaci gwamnan akan ya gabatar masa da hujjar ba shi kuɗi akan takarar da ya ke yi.
Kawo yanzu dai Labarai24 ba ta samu wata sanarwa daga A.A Zaura ko Inuwa Ibrahim Waya ɗin dangane da abin da Gandujen ya yi.