Abdullahi Muhammad" />

Ganduje Ya Jinjinawa Jama’ar Kano Bisa Sake Zabar Buhari

Gwamna Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana farin cikinsa bisa Nasarar da dan Takarar Jam’iyyar APC na shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu na sake darewa kujerar shugabancin kasa karo na biyu daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa 29 ga watan Mayun shekara ta 2023, haka kuma Ganduje ya jinjinawa sabon salon da jama’ar Kano suka dauka a lokacin zaben, Gwamnan Ganduje ya kuma yabawa Jama’ar Kano bisa bai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kuri’ar da ba wata Jiha a Kasar nan ta bashi irinta, inda Buhari ya samu kuri’a Miliyon 1,464,768 wanda ke zaman kaso 78% a Jihar Kano kadai.
Sakamakon zaben shugaban kasar ya nuna cewar Muhammadu Buhari ya samu kuri’a Miliyon 15,191,847 a tsakanin jihohin kasarnan 37 harda Abuja, wanda hakan tasa ya kayar da abokin takararsa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar wanda ya samu kuri’a Miliyon 11,262978 Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje na wannan Jawabi ne ga masu ruwa da tsaki a Jihar Kano lokacin da suke tattauna sakamakon zaben da ya gudana, Ganduje ya ci gaba da cewa wannan gagarumin zabe da Jama’ar Kano suka yi ne ke nuna irin kaunar salon shugabancin Muhammad Buhari. Don haka yace ya zama wajibi mu godewa al’ummar Jihar Kano wadanda suka fito kwansu da kwarkwata suka baiwa Shuaban kasa Muhamadu kuri’un daba irinsu a lokacin zaben da ya gudana.
Hakazailka Gwamna Ganduje ya karra jinjinawa Jama’ar Kano bisa fitowar da suka yi don haka sai ya bukace su dasu kara irin wannan fitar dango domin kadawa ‘yan takarkarun jam’iyyar mu ta APC a lokacin zaben ranar 9 ga watan feburairin shekara ta 2019. Yin hakan zai kara baiwa wannan gwamnati damar ci gaba kwararawa Kanawa ayyukan alhairi.

Exit mobile version