Connect with us

LABARAI

Ganduje Ya Kafa Kwamiti Don Gano Yaran Da Aka Sace

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar zartaswa na bincike kan yaran da aka sace a Jihar ta Kano.

A wata hira da manema labarai suka yi da mai baiwa gwamnan shawara kan harkokin yada labarai Salihu Tanko Yakasai da safiyar yau Lahadi ya ce; Abdullahi Umar Ganduje ya nada mai shari’a Wada Abubakar Umar Rano, a matsayin shugaban kwamitin.

Ya kara da cewa, mutanen da suka gabatar da bincike game da sace yaran sune aka kara nadawa cikin kwamitin zartaswar domin zartar da abubuwan da suka zayyana da in an bi za su iya kawo karshen faruwar lamarin.

Daga cikin shawarwarin da kwamitin binciken da aka kafa a watan Oktoban shekarar 2019 ya bayyana yadda za a iya nemo sauran yaran da ake zargin har yanzu ba akai ga ganowa ba.

Da yake kaddamar da kwamitin Gwamna Ganduje ya ce; Matukar laifuka na karuwa to kuma aikinku zai ci gaba da karuwa, ba mason muga an yi watsi da wannan rahoton da kuka tattaro shi yasa muka sahale muku cewa ku zartas da shi.”

Cikin wannan kwamitin akwai jami’an ‘yan sanda da masu fafutukar kare hakkin dan adam da kungiyoyin fararen hula da wakilan kungiyar malaman Musulunci da na kungiyar Kiristoci da dai sauransu.
Advertisement

labarai