An yammacin ranar Juma’ar nan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aiko da jirgi sukutum daga Abuja tare da umarnin lallai a lallashi Sanata Shekarau ya dakatar da fiacewa daga Jam’iyyar APC.
Tunda farko dai gwamnan ya aike da wata tawagar Jami’an gwamnatin Kano da ta hada da Kwamishinan yada labaran Jihar, Muhammad Garba tare da shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan Nijeriya Alasan Ado Doguwa kan su je gidan Shekarau su lallashe shi su kuma isar masa da sakon shugaban kasa.
- 2023: Shekarau Ya Yi Watsi Da Bukatar Gawuna Ta Hana Shi Ficewa Daga APC Zuwa NNPP
- 2023: Ban Gama Yanke Shawarar Ficewa Daga APC Ba Tukunna —Sanata Shekarau
Sai dai Sanata Shekarau din ya yi watsi da bukatar gayyatar ta shugaban kasar cewa ba zai je Abuja don tattaunawa kan batun sulhu da tsagin na su Gandujen ba.
Bayan ficewar tawagar gwamnatin daga gidan Shekarau ba jimawa kwatsam sai suka dawo gidan Shekarau da Gwamna Ganduje suka kuma bukaci ganawa da Sanata Shekarau kan ya amsa gayyatar zuwa sulhun a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Majiyarmu daga gidan Sanata Shekarau din ta ce Ganduje da Shekarau sun saka labule sun tattauna na tsawon mintuna 20, sai daga bisani ya fito daga gidan zuwa fadar gwamnatin Kano.
Wani makusancin Sanata Shekarau ya shaida mana cewa zai gana da ‘yan kwamatinsa gabanin yanke hukunci amsa gayyatar sulhun zuwa Abuja don kawo karshen sa-toka-sa-katsin da ake bugawa a Jam’iyyar APC ta Jihar Kano.
Mun samu labarin cewa tun misalin karfe 05:30 na yamma aka turo jirgi daga Abuja kan ya dauki Sanata Shekarau da Gwamna Ganduje don ganawa da Ganduje da shugaban kasa kan sulhunta bangarori biyun da suke tafka rikicin siyasar cikin gida a Jam’iyyar APC ta Jihar Kano.
Majiyarmu ta ce tuni Sanata Shekarau din ya shiga ganawa da magoya bayansa kan bukatar ta sulhun da kuma batun sauya sheka zuwa Jam’iyyar NNPP ta Sanata Rabi’u Kwankwaso da ake saran gobe Asabar zai aiyana shiga Jam’iyyar.
Da daren yau Juma’a ake saran Sanata Rabi’u Kwankwaso zai yi wata ganawar sirri da Sanata Shekarau a gidansa da ke unguwar Mundubawa cikin karamar hukumar Nassarawa.
Abun tambayar anan shin Sanata Shekarau zai amsa batun sulhun rikicin siyasarsa da APC ko zai gana da Kwankwaso kan yuyuwar aiyana shigarsa Jam’iyyar NNPP?
Ku ci gaba da kasancewa tare da mu don jin halin da ake ciki kan wannan batu.