Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin shugaban kwamitin gudanarwar asibitocin nan biyu na kwararru tare da mambobinsu.
Jawabin haka na kunshe cikin jawabin da babban daraktan yada labaran Gwamnan Jihar Kano Abba Anwar ya rattabawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Kano wanda kuma nadin ya fara aiki nan take.
A cewar Gwamna Ganduje an yi wannan nadi ne bisa cancanta, don haka sai ya bukace su da a ko da yaushe su kasance masu yiwa Jihar Kano hidima a farko kafin komai. Kamar yadda yake cikin kunshin dokokin gudanar da harkokin asibitocin biyu.
“Ku tabbatar da ganin kun gudanar da ayyukanku yadda ya kamata, tare da kulawa da matsayin wadannan asibitoci. Wannan Gwamnati na baiwa harkokin lafiya kulawa ta musamman, don haka ku tabbatar da ganin ana tafiya kamar yadda tsarin yake a duniya baki daya,” inji shi.
Wadanda aka nada din sun hada da Prof Yusuf D. Sabo a matsayin shugaba, Dr Hadiza Ashiru matsayin babbar jami’a, Dr Abdullahi Kauranmata wakilin ma’aikatar lafiya, Zahraddeen Lawan wakilin ma’aikatara kudi da Eng. Murtala A. Garba wakili daga ma’ aikatar kiyaye ka’idojin aiki.
Sauran su ne Hajiya Bilkisu Maimota, wakiliya daga ofishin sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Hajiya Halima Ali Aware wakiliya daga ma’aikatar zuba jari da kadarori Gwamnati, Hajiya Hafsat Kolo Wakiliyar kungiyoyi masu zaman kansu,, Alhaji Kabiru Nassarawa wakilin kamfanoni masu zaman kansu, Sanusi Ali Sadik daga ANAN/ICAN reshen JiharKano da Madam Comfort Onwuegbuna da ke wakilta kungiyoyin mata.
Gwamna Ganduje ya bukace su da ako da yaushe yi duk mai yiwuwa domin kara inganta hrkokin lafiya a Jihar Kano. “Sannan ku taimakawa wannan Gwamnatin JIhar Kano domin rike kambunta na Jihar da ke sahun gaba a fadin kasarnan wajen samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya.”