Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya ce ya kamata a samar da dokar da za ta haramta kiwon shanu daga arewa zuwa kudancin kasar.
An ruwaito Ganduje na fadin haka a garin Daura da ke Jihar Katsina, lokacin da shi da sauran gwamnonin jam’iyyar APC suka ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ganduje ya ce matukar ba a dakatar da zirga-zirgar shanu tsakanin yankunan biyu ba, to ba za a taba kawo karshen rikicin manoma da makiyaya ba. Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta samar da wurin kiwo ga masu kiwo a wani daji da ke nusa da iyakar Kano da Katsina.