Connect with us

LABARAI

Ganduje Ya Samu Goyon Bayan ‘Yan Adaidaita Sahu A Zabe Mai Zuwa

Published

on

Mataimaki na musammam ga Gwamnan Kano a kan makanikai Injiniya Idris Hassan Gwawuna ya bayyana cewa, tururuwa da ake na koma wa cikin jam’iyyar APC a jihar Kano sakamako ne na irin kulawa da ci gaban al’umma da Gwamnatin Kano karkashin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje yake ga ci gaban jihar.
Alhaji Idris wanda ya bayyana hakan da yake zantawa da wakilimmu a wajen bikin karbar yan baburan adaidaita sahu da suka bar jam’iyyar PDP da tsagin kwankwasiyya suka shigo cikin APC da ka gudanar a rufaffaen dakin wasa na Sani Abacha dake kofar mata.
Ya ce, sakamakon irin gudummuwa da Ganduje ke bayar wa ga ci gaban Kano kullum jam’iyyar APC sai kara karbuwa take ana ta shigo wa cikin ta daga bangarori daban-daban na al’umma wannan ce ma tasa masu tuka baburan mai taya uku dubbansu suka shigo cikin jam’iyyar dan mara wa Gwamnatin Buhari da Ganduje baya.
Mataimaki na musamman ga Gwamna Ganduje a kan makanikai ya kara da cewa irin kulawa da suka samu a karkashin ofis dinsa kawa wani babban al’amari ne dayaja hankalinsu suke dawo wa tafiyar Ganduje domin kuwa anyi musu tallafi kala-kala baya ga daukar nauyin makanikansu aka koya musu gyaran mashina mai taya uku.
Injiniya Idris Hassan ya ce, har kasar indiya sukaje suka dauko jami’ai a kanfanin Bajaj da TBS suka zo suka koya musu gyara aka kuma ba su kyautar kayan gyara a akwati aka bai wa direbobin kyautar tayoyi da kuma man juye da sauran abubuwa da dama da ake musu, sannan kuma aka dauke musu haraji da suke biya.
Injiniya Idris Hassan Gawuna ya yi kira ga masu gudanarda sana’ar tuka babaura masu taya uku a jiharsu ci gaba da bai wa Gwamna Ganduje Goyon baya dan ci gaba da habakar sana’arsu tare da kiransu a kan su tabbatar sun karbi katin zabe domin shi ne abin da za su yi amfani da shi wajen sake tabbatar da Gwamnatin APC a jihar Kano da kasa baki daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: