Daga Khalid Idris Doya,
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sha alwashin cewa, zai mutunta tanade-tanaden dokar kasa a matsayinsa na gwamna ya sanya hannu kan hukuncin kisa ba tare da bata wani lokaci ba muddin kotu ta zartar da hukuncin kisa ga malamin da ya yi kisan gilla wa dalibarsa ‘yar shekara 5 a duniya wato Hanifa Abubakar Abba.
Ganduje, ya ce ko minti guda ba zai wani jira ba a duk lokacin da kwafin hukuncin ya zo gabansa zai sanya hannu ba tare da jiran-jiran ba.
Wata sanarwar da babban sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar ya fitar, ya habarto gwamnan na yin wannan alkawarin ne a lokacin da ya jagoranci tawaga da ta kunshi shi kansa, mataimakin gwamna, Dakta Nasuru Yusuf Gawuna, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar, Labaran Abdul Madari da sauran jami’an gwamnati zuwa ziyarar jajantawa ga iyalan mamaciyar a gidansu da ke Dakata/Kawaji a ranar Litinin.
Gwamnan ya ce: “Mun samu tabbaci daga kotun da ke shari’ar wannan lamarin cewa tabbas za a wanzar da adalci.
“Ina ba ku yakini, da zarar kotu ta tabbatar da laifin da ake zarginsa da shi zai bakunci lahira ba tare da bata wani lokaci ba. A matsayinmu na gwamnati tunin ma muka fara shirye-shiryen aiwatar da hakan, kotu kawai muke jira ta kammala aikin ta.”
Ganduje ya cigaba da cewa kwansitushin ya riga ya daddale hukuncin kisa gwamna ne ke da karfin ikon sanya hannu wajen zartaswa, don haka ne ya bada tabbacinsa da cewa, a kan wannan lamarin na kisan gilla da aka yi wa karamar yarinya Hanifa ko ‘Sakon guda’ ba zai Jira ba zai sanya Hannu domin mai laifin ya dandani zafin mutuwa shi ma.
Ya jawo hankalin alkalin da ke shari’ar da ya hanyarta gudanar da shari’ar, ya Kuma dauki alkawarin kula da iyalan mamaciya Hanifa da fatan Allah ya sanyata cikin masu ceton iyayenta.
Ya nuna kisan a matsayin abin kaito da Allah wadai, sai ya ce dole za su san yadda kuma za su yi da makarantar su marigayiyar.