Umar A Hunkuyi" />

Ganduje Ya Sha Alwashin Canza Wa Hukumar Hizba Fasali

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya ce, Hukumar Hisba ta canza daga ainihin turban da aka kafata, domin haka tana da bukatar a sake mata fasali baki-dayanta. Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin sanya hannu a kan sabuwar dokar nan ta iyali a Jihar ta Kano.
Ganduje ya yi wannan maganan ne a Kano, bayan da aka kammala daurin auren Zawarawa 70. “Gwamnati ba za ta ci gaba da lamunta ba, kan irin tabargazan da shugabannin hukumar ta Hisba ke tafkawa.
“Shugabancin da ake sa ran zai gudana ne a karkashin dokokin Alkur’ani da Sunnan Ma’aikin Allah (SAW), amma sai ga shi ana gudanar da shi a bisa ra’ayi da son ran wasu daidaiku. Kuma abin takaici, su shugabannin hukumar ta Hisba a cikin jahilcin su, sai suna zaton matsawa mutane shi ne daidai.
Sam gwamnati ba za ta lamunci hakan ba, tilas ne ta yi maganin lamarin, in ji Ganduje. “Akwai abin da gwamnati ya kamata ta yi, Masarautar Kano ma tana da abin da ya kamata ta yi, haka nan baki-dayan al’umma, kowa yana da rawar da ya kamata ya taka.
A matsayin Hisba na hukuma, an kafata ne domin ta tabbatar ana bin doka sau da kafa. Ya ce, tilas ne a sakewa Hisba fasali ta yanda za ta tabbatar da ana bin sabuwar dokar ta iyali sau da kafa. Sarkin Kano, Mai Girma Muhammadu Sanusi II, wanda shi ne ya bullo da sabuwar dokar ta iyali a Jihar ta Kano, ya ce, an kafa dokar ne domin ta magance matsalolin da suka shafi Aure, har da batun yawan mutuwar auren da ake yi, matsalolin Gado, da kuma hakin da ke kan ma’auratan bayan rabuwar Auren na su da makamantan hakan, In ji Sarkin.
Auren Zawarawan da aka daura shi ne karo na hudu a Kano din. jimillan ma’aurata 1,500 ne aka yi wa irin wannan daurin Auren.

Exit mobile version