Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano
Majalisar zartarwa ta Jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyaon kusan tara (N8, 980, 303, 460.63) domin gina gada wadda ake sa ran sawa sunan Shugaban kasa Muhammadu Buhari wadda ke kan Titin Maiduguri da ke ƙwaryar birnin na Kano.
Majalisar ta amince da kashe kudin ne jim kadan bayan kammala zamanta na mako-mako a dakin taro na Africa House da ke fadar Gwamnatin Jihar Kano.
Kwamishinan Yada Labarai Malam Muhammad Garba ya ce wannan yunkuri na cikin burin Gwamnatin Dakata Abdullahi Umar Ganduje na gina tituna da hanyoyi domin mayar da Kano “hamshakin birni” da kuma habaka harkokin kasuwanci.
A cewarsa: “Kasancewar Kano birni mai tasowa kuma cibiyar kasuwanci a Nijeriya, Kano na samun karuwar ‘yan kasuwa da ke shigowa, abin da ya sa ake bukatar sake tsarawa tare da habaka tituna don su iya daukar masu zirga-zirga a cikinsa.”
A makon da ya gabata ne tsohon Gwamna kuma jagoran adawa a Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki aikin gadar, yana mai cewa “mutanen Kano sun fi bukatar ilimi” ba gada ba.
Kazalika, kwamishinan ya ce majalisar ta amince da kashe Naira Miliyon 44,300,000 domin yi wa Kwalejin Harkokin Noma ta Audu Bako da ke karamar Hukumar Dambatta gyare gyare.