Ganduje Ya Yi Alkawarin Ci Gaba Da Bunkasa Jihar Kano

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin cigaba da gudanar da ayyukan bunkasa jihar Kano tare da tarin ayyukan da al’umma masu zuwa nan gaba za su yi alfahari da shi.

Ganduje ya yi wannan bayanin ne a taron karrama shi da kungiyar ‘yan jarida ta yi a garin Kano.

Ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarinta na samar wajen samar wa da ‘yan jihar romon dimokradiyya a fadin jihar.

Ganduje, na daga cikin mutum biyar da kungiyar ta karrama, ya kuma ce, bayar da ilimi kyauta na daga cikin burinsa gwamnatinsa na ba yaran jihar damar samun ilimi ba tare da banbanci ba.

Ya kuma ce, gwamnatinsa ta shirya shirgar da tsarin karatun almajirai a cikin tsarin makarantun boko da kuma ganin an stayar da fitar da yara ke yi daga makaranta.

“Yawanci yaran da ke gararamba a da kuma ake fita daga makaranta ba wai ‘yan jihar Kano ne kawai, amma dole mu yi wani abu akansu saboda ai suma yan Njeriya ne,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa, karramawa za ta karfafa masa na kara kaimi wajen ayyukan da yake yi na bunkasa jihar Kano.

Ya kuma bukaci yan jarida su cigaba da wasta ayyukan gwamnatin jihar tare da yin korafin a inda ya kamata, don kuwa ana samun karin ilimi a inda ake yin suka mai ma’ana.

Tunda farko, shugaban kungiyar ‘yan jaridar, Malam Ibrahim Garba-Shu’aibu ya ce, an shirya karamawar ne don yaba wa masu kokari a dukkan fannoni daban daban na rayuwar al’umma da fatan karfafasu a kana bin da suke yi.

Wadanda aka karrama sun hada da Farfesa Hafsat da Farfesa Umar Garba Dambatta, shugaban hukumar NCC, da Alhaji Isyaku Umar-Tofa da kuma Dakta Jamil Gwamna.

Exit mobile version